Wane ne zai lashe Ballon d'Or a bana?

..
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

A yau ne za a sanar da wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or a birnin London, amma wa zai iya lashe kyautar a bana?

Masu hasashe sun sanya ƴan wasan gefe na Sifaniya, Lamine Yamal, da kyaftin ɗin Ingila, Harry Kane, a matsayin waɗanda suka fi sauran 'yan takara ƙarfi wajen lashe babbar kyautar.

Yamal ya taimaka wa Barcelona wajen lashe gasar La Liga, sannan ya samu nasara tare da tawagar Sifaniya a gasar cin Kofin Duniya, yayin da Kane ya zura ƙwallaye 73 a raga tare da zakarun Jamus Bayern Munich da kuma tawagar Ingila.

Sauran waɗanda ake ganin suna da damar lashe kyautar sun haɗa da gwarzon ɗan wasan Argentina da Inter Miami, Lionel Messi, wanda ya lashe Ballon d'Or sau takwas, da kuma ɗan wasan gaba na Faransa da Real Madrid, Kylian Mbappe.

Ko kuwa ɗaya daga cikin 'yan wasan Paris Saint-Germain da suka lashe Gasar Zakarun Turai a jere ne zai ɗauki kyautar?

Sashen wasanni na BBC ya tambayi wasu daga cikin masana ƙwallon ƙafa da ke aiki da sashen su bayyana wanda suke ganin ya fi cancantar lashe Ballon d'Or na bana.

Lamine Yamal

Lamine Yamal

Masanin ƙwallon ƙafa na Turai, Guillem Balague, ya ce ba ya ganin akwai yiwuwar ɗan wasan da ba daga PSG ko Sifaniya ba ya lashe kyautar Ballon d'Or ta bana, lamarin da ya sa ya cire Kylian Mbappe daga cikin manyan waɗanda yake ganin za su iya ɗaukar kyautar.

Ya ce PSG na da ƴan wasa da dama da suka cancanci a ba su kyautar, ciki har da Fabian Ruiz, Khvicha Kvaratskhelia, Ousmane Dembele da Vitinha, abin da a cewarsa zai iya sa ƙuri'un masu zaɓe su rarrabu a tsakaninsu.

Balague ya ƙara da cewa akwai ɗan wasa ɗaya kacal daga Sifaniya da yake ganin ya fi kowa cancanta, wato Lamine Yamal.

A cewarsa, Yamal ya nuna bajintar ɗaiɗaiku a filin wasa, ya taimaka wajen lashe manyan kofuna tare da ƙungiyarsa da ƙasarsa, sannan kuma yana da wata irin ƙima da kwarjini na musamman.

"Don haka shi nake ganin zai lashe kyautar," in ji Balague.

Khvicha Kvaratskhelia

Khvicha Kvaratskhelia
Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masanin ƙwallon ƙafa na Turai, Julien Laurens: Ya ce a ganinsa Khvicha Kvaratskhelia ne ya fi kowa taka rawar gani a Turai a kakar wasan da ta wuce, musamman a Gasar Zakarun Turai inda ya nuna bajinta sosai.

Ya ce ɗan wasan ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa ƙungiyarsa ta lashe wani babban kofi, inda ya samu fenaritin da aka ci a wasan ƙarshe, sannan ya zura ƙwallaye a wasannin daf da na ƙarshe, kwata-fainal da kuma zagaye na biyu na gasar.

Laurens ya ce Kvaratskhelia ya yi fice musamman a manyan wasannin da ake buƙatar fitattun ƴan wasa su taka rawar gani, abin da ya sa yake ganin ya cancanci lashe Ballon d'Or a matsayin mafi kyawun ɗan wasa a duniya har zuwa Gasar cin Kofin Duniya.

Sai dai ya ce da alama ba zai lashe kyautar ba, domin Lamine Yamal na da farin jini sosai saboda irin salon wasansa mai ƙayatarwa da burge masu kallo.

A cewar Laurens, duk da cewa Sifaniya ta lashe Kofin Duniya, Yamal bai yi fice sosai a gasar ba, haka kuma Barcelona ta fice da wuri daga Gasar Zakarun Turai.

Duk da haka, ya ce salon wasansa na iya sa ya lashe kyautar, amma a ganinsa Kvaratskhelia ne ya fi cancanta.

Tsohon ɗan bayan Liverpool da Blackburn, Stephen Warnock: Ya ce yana ganin Lamine Yamal ne zai lashe kyautar Ballon d'Or saboda rawar da ya taka wajen taimaka wa Sifaniya lashe Kofin Duniya.

Ya ce idan za a ambaci sauran 'yan takarar da ke sahun gaba, zai saka Michael Olise a ciki, amma a ra'ayinsa Khvicha Kvaratskhelia ne ya fi kowa cancanta.

"A gare ni Kvaratskhelia abin mamaki ne. Ina matuƙar jin daɗin kallon wasansa. Ya yi tasiri sosai a PSG, kuma kakar wasan da ta gabata ya kasance cikin ƙwararrun 'yan wasan Turai," in ji Warnock.

Sai dai ya ce ba ya tunanin ɗan wasan zai samu isassun ƙuri'u, ganin cewa ƙasarsa ta Georgia ba ta shiga Gasar Kofin Duniya ba.

Shi ma baƙon shirin Euro Leagues na BBC Radio 5 Live kuma ɗan jaridar The Athletic, Rory Smith: Ya ce mai yiyuwa ne Yamal ya lashe kyautar saboda yawanci ana bai wa ɗan wasan da ya taka rawa wajen lashe babbar gasa, wato Kofin Duniya.

Sai dai Smith ya ce a ganinsa Yamal bai kasance mafi muhimmancin ɗan wasan Sifaniya ba, amma shahararsa da hazaƙarsa za su iya sa ya zama wanda ya ɗauki kyautar.

"Da ni ne zan zaɓa, zan bai wa Kvaratskhelia kyautar. Ya kasance ɗaya daga cikin ƴan wasan da suka fi ƙayatarwa a ƙwallon kulob-kulob na Turai na tsawon lokaci, kuma ya taka muhimmiyar rawa a ƙungiyar PSG da ta kare kambunta na Gasar Zakarun Turai.

"Haka kuma, bana ganin ya kamata ɗan wasa ya rasa damar lashe kyauta saboda kawai ƙasarsa ba ta cikin waɗanda ke fafatawa wajen lashe Kofin Duniya," in ji Smith.

Harry Kane

Harry Kane

Tsohon ɗan wasan gaba na Ingila, Alan Shearer: Ya ce Harry Kane ne ya kamata ya lashe kyautar Ballon d'Or.

Ya ce alkaluman Kane a watanni 12 zuwa 18 da suka gabata tare da Bayern Munich da kuma tawagar Ingila sun kasance masu ban mamaki matuƙa.

"Saboda irin waɗannan nasarori da bajintar da ya nuna, ya cancanci lashe kyautar," in ji Shearer.

Shi ma tsohon ɗan wasan tsakiya na Ingila, Danny Murphy: Ya zaɓi Kane a matsayin wanda ya kamata ya ɗauki Ballon d'Or.

Murphy ya ce Kane ya nuna ƙwarewa ta musamman wajen zura ƙwallaye a raga, kuma kakar wasan da ta gabata na daga cikin mafi kyau a rayuwarsa ta ƙwallo.

"Ya yi fice sosai tun bayan zuwansa Bayern Munich, inda ya dace da salon ƙungiyar cikin sauri. A ganina, shi ne mafi kyawun ɗan wasan gaba na tsakiya a duniya cikin watanni 12 da suka gabata," in ji Murphy.

Shi kuwa tsohon ɗan wasan Tottenham da Crystal Palace, Andros Townsend: Ya ce Kane ya cancanci lashe kyautar bayan ya zura ƙwallaye 73 a wasanni 65, ciki har da 36 a Bundesliga.

Townsend ya ce Kane ya taimaka wa Bayern Munich wajen lashe kofunan gasar liga da kofin cikin gida, sannan ya ci ƙwallaye 14 a Gasar Zakarun Turai inda ya jagoranci ƙungiyar zuwa wasan kusa da na ƙarshe.

Haka kuma ya zura ƙwallaye shida a gasar Kofin Duniya tare da taimaka wa Ingila zuwa wasan kusa da na ƙarshe, abin da ya sa ya bayyana shekararsa a matsayin ta musamman

Kylian Mbappe

Kylian Mbappe

Ɗan wasan gaban na Faransa na daga cikin waɗanda ake ganin za su iya lashe kyautar saboda bajintar da ya nuna a kakar da ta gabata.

A Gasar Kofin Duniya da ta gabata ɗan wasan gaban ya kafa bajintar zama ɗanwasan da ya fi kowa zura ƙwallo a tarihin Gasar Kofin Duniya, inda ya ci 22.

Haka kuma shi ne ɗan wasan da ya fi kowa zura kwallo a gasar ta bara, sannan ya fi kowa cin kwallo a gasar La Liga da ta wuce.

To sai dai ana ganin rashin coin kofi a bara ka iya zame masa kaliubale wajen lashe kyautar a bana.