Abubuwa shida kan wasan Barca da Inter a Champions League

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Kimanin shekara 15 tun bayan da aka yi karawar daf da karshe a Champions League tsakanin Barcelona da Inter Milan, yanzu za su sake haɗuwa ranar Laraba.

Inter Milan ce ta kai zagayen karshe a 2010, sai dai wannan karon Barcelona na fatan lashe kofin bana da zarar ta fuskanci Arsenal ko Paris St Germain a watan gobe.

Sai dai, Barca da Inter sun fuskanci juna a gasar ta zakarun Turai a 2022/23, inda ta Italiya ta yi nasara 1-0 cikin Oktoban 2022 a wasa na biyu suka tashi 3-3 a Sifaniya.

Wannan shi ne karon farko da Barcelona ke fatan kai wa karawar karshe a Champions League, tun bayan da ta lashe na biyar jimilla a 2015.

Inter Milan na fatan yi wa Barcelona fancale a gasar ta zakarun Turai a bana, wadda ta yi waje da Bayern Munich a zagayen kwata-fainal.

Sai dai, ƙungiyar da ke buga Serie A ta kwan da sanin cewar a wasa uku baya da ta je Sifaniya ta kasa yin abin kirki.

Ga jerin batu biyar kan wasan Barcelona da Inter Milan:

Sun kara sau 16 a tsakaninsu

Barcelona da Inter Milan sun fuskanci juna sau 16 a babbar gasar zakarun Turai, inda ƙungiyar Sifaniya ta yi nasara takwas da canjaras biyar aka doke ta wasa uku.

Wasan karshe da suka haɗu a gasar shi ne a cikin rukuni a 2022/23 a Champions League, inda Inter ta ci 1-0 suka tashi 3-3 a cikin watan Oktoba.

Filin Barcelona 'ya fi karfin' Inter Milan

Barcelona ta yi wasa shida ba tare da an doke ta ba a gida a wasan da ta yi da Inter Milan a baya a Champions League, wadda ta yi nasara biyar da canjaras ɗaya.

Nasara biyar da Barcelona ta yi a kan Inter Milan a gida ta yi kan-kan-kan da yawan yadda ta doke AC Milan karo biyar a gasar ta zakarun Turai.

Sai dai Barcelona ta karɓi bakuncin Chelsea karo bakwai a gasar ta zakarun Turai a gida ba tare da an doke ta ba, shi ne karawar da ta ci da yawa a gasar.

Tarihi ga Inzaghi

Kocin Inter Milan, Simone Inzaghi, zai ja ragamar wasa na 50 a Champions League ranar Laraba a Sifaniya, zai zama mai horarwa na bakwai daga Italiya da ya yi wannan ƙwazon - yanzu yana kan-kan-kan da ƙasar Sifaniya mai masu horar da tamaula shida a tarihi.

Inzaghi, ya kuma ci wasa 25 daga karawa 49 - shi ne koci daga Italiya mai wannan bajintar a Champions League, ya haura Marcello Lippi, wanda ya yi nasara 25.

Martinez dodon raga

Lautaro Martínez ya zura ƙwallo a raga a dukkan wasanni biyar a baya da ya buga a Champions League.

Da zarar ya ci Barcelona ranar Laraba, zai zama ɗan Kudancin Amurka da ya zura ƙwallo a raga a wasa na shida a jere a gasar, bayan ƙwazon Edison Cavani mai bakwai tsakanin Nuwambar 2016 zuwa Oktoban 2017.

Yamal da Raphinha na wuta

Ƴan wasan Barcelona, Lamine Yamal da Raphinha sun zazzaga ƙwallaye 16 a raga a tsakaninsu a Champions League ta bana.

Raphinha yana da kwallo 12 ya bayar da bakwai aka zura a raga, shi kuwa Yamal ya ci kwallo huɗu ya bayar da uku aka zura a raga.

Haka kuma sune kan gaba a yawan samar da damarmaki da yawa a lokacin wasannin, kowannensu ya ƙirkiri dama 16.

Ko Flick zai maimaita lashe kofi uku rigis?

A kakar 2019/20, Flick ya ja ragamar Bayern Munich ta lashe kofi uku da ya haɗa da na Bundesliga da DFB-Pokal da kuma UEFA Champions League.

Flick, wanda ya koma Barcelona kan fara kakar nan, ya ɗauki Spanish Super Cup a watan Janairu, sakamakon doke Real Madrid 5-2 a watan Janairu a Saudiyya.

Haka kuma ya ƙara yin nasara a kan Real Madrid a Copa del Rey da ci 3-2 ranar Asabar a Sevilla - kenan yana fatan lashe Champions League a kakar nan.