Lafiya Zinariya: Illolin na'urorin fasahar zamani ga yara
Lafiya Zinariya: Illolin na'urorin fasahar zamani ga yara
An wallafa
Cigaban fasahar zamani da ake samu na taimakawa wajen bunƙasar al'umma, sai dai hakan ta wani ɓangare na janyo haɗari ga lafiyar ƙwaƙwalwa da jikin yara ƙanana.
Yawan amfani da wayar tafi-da-gidanka, da kwamfutoci, da wasan kwamfuta da sauransu na da illa ga lafiyar yara idan suna amfani da su fiye da kima.
kaɗan daga cikin illolin sun hada da dakushewar kwakwalwa, teɓa, tsangwama a tsakanin yara saboda dakushewar ƙwaƙwalwa.
Haka kuma yawan amfani da na'urorin fiye da kima na iya janyo matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa da rage kaifin ido.
Yawan wasa da na'urorin kan rage wa yara shiga sa'o'insu don su yi wasa, lamarin da ke da muhimmanci ga girman yaro cikin ƙoshin lafiya.