Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Newcastle ta lashe babban kofin gida karon farko a shekara 70
Newcastle United ta yi nasarar lashe Carabao Cup na bana, bayan doke Liverpool 2-1 ranar Lahadi a Wembley.
Newcastle ta fara cin ƙwallo ta hannun Dan Burn daga baya Alexander Isak ya kara na biyu.
Liverpool ta zare ɗaya ta hannun Federico Chiesa, kafin a karɓi cin sai da aka jira na'urar VAR ta fayyace, daga baya aka bayar da ƙwallon daf da za a tashi wasan.
Wannan shi ne wasa na uku da suka kara a kakar nan, inda aka tashi 3-3 a gidan Newcastle, Liverpool ta yi nasara 2-0 a Anfield a wasa na biyu.
Wasa uku a bana tsakanin Liverpool da Newcastle:
Carabao Cup ranar Lahadi 16 ga watan Maris 2023
- Liverpool 1 - 2 Newcastle
Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairun 2025
- Liverpool 2 - 0 Newcastle
Premier League ranar Laraba 4 ga watan Disambar 2024
- Newcastle 3 - 3 Liverpool
Newcastle United ta lashe babban kofi tun bayan Inter City Fair Cup a 1968/69, kuma babban kofin gida tun bayan lashe FA Cup a 1954/55.
Eddie Howe ya zama kociya ɗan Burtaniya da ya ɗauki ko dai FA Cup ko kuma Carabao tun bayan Harry Rednapp a Portsmouth a 2008.
A karon farko Mohamed Salah na Liverpool ya kasa cin ƙwallo ko ya bayar a zura a raga a karawar da ya buga minti 90.
Newcastle mai kwantan wasa tana ta shida a teburin Premier League da maki 47, bayan cin wasa 14 da canjaras biyar aka doke ta tara daga ciki.
Liverpool, wadda tun farko ta sa ran lashe kofi huɗu a bana, Plymouth ta yi waje da ita a FA Cup, sannan Paris St German ta fitar da ita a Champions League, sai Newcastle da ta ɗauki Carabao Cup.
Sai dai Liverpool za ta tsira da Premier League a bana, wadda take ta ɗaya a kan teburi da maki 70 da tazarar maki 12 tsakani da Arsenal ta biyu.
Liverpool na sa ran lashe Premier League na biyu bayan 2020 kuma na 20 jimilla kamar yadda Manchester United take da shi.