An dakatar da Slot wasa biyu da biyan tarar £70,000

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

An dakatar da kociyan Liverpool, Arne Slot wasa biyu, sakamakon jan katin da aka yi masa a wasan Premier League da Everton.

Alkalin wasa, Michael Oliver ne ya yi masa jan katin, bayan tashi 2-2 a Goodison Park ranar 12 ga watan Fabrairu.

Kenan Slot ba zai ja ragamar wasan da Liverpool za ta kara da Newcastle United ranar Laraba da wanda za ta je Southampton ranar 8 ga watan Maris ba.

Amma zai jagoranci Liverpool wasan ƴan 16 a Champions League da Paris St Germain ranar 5 ga watan Maris.

Haka kuma Slot zai biya tarar £70,000, bayan da ya amince da tuhumar da aka yi masa tun farko.

Haka shima mataimakin Slot, Sipke Hulshoff an dakatar da shi fafatawa biyu da biyarn tarar £7,000.

An kuma ci tarar Everton £65,000 da kuma ƙarin £50,000, saboda an same su da laifin kasa tsawatarwa ƴan wasansu.

Tun farko Slot ya yi cacar baki da mataimakin rafli, daga nan ya je ya yi hannu da Oliver, wanda nan take ya yi masa jan kati.