Arsenal da Bayern na zawarcin Williams, Chelsea ta amince da cinikin Essugo

Asalin hoton, Getty Images
Bayern Munich ta sabunta zawarcinta kan ɗan wasan Athletic Bilbao da Sifaniya, Nico Williams mai shekara 22, amma za ta fuskanci kalubale daga Arsenal da ita ke farautar ɗan wasan. (Bild)
Ɗan wasan Newcastle da Sweden, Alexander Isak mai shekara 25, ya ce zai tattauna da ƙungiyarsa kan sabunta yarjejeniyarsa a lokacin bazara. (Mail)
Chelsea ta amince da yarjejeniyar saye ɗan wasan tsakiya a Portugal, Dario Essugo mai shekara 20 daga Sporting kan £21m, bayan cikar wa'adin zaman aron da yake yi a Las Palmas. (A Bola - in Portuguese)
Real Madrid na son ɗauko ɗan wasan baya a Tottenham da Argentina, Cristian Romero mai shekara 26, da kuma mai bugawa Everton da Ingila, Jarrad Branthwaite mai shekara 22, domin karfafa bayanta. (Teamtalk)
Everton na shirya yada za ta saye ɗan wasan gaba a Moroko, Hamza Igamane mai shekara 22 daga Rangers a wannan kaka. (Football Insider)
Liverpool za ta fuskanci kalubale daga Arsenal a cinikin ɗan wasan Jamus, Leroy Sane mai shekara 29, idan kwantiraginsa ya kare a Bayern Munich a wannan kaka. (Fichajes - in Spanish)
Brighton na sa ran karban tayin sama da £20m kan ɗan wasan tsakiya daga Sweden, Yasin Ayari mai shekara 21, wanda ya ja hankalin Borussia Dortmund da AC Milan. (Football Insider)
Barcelona a shirye take ta shiga tattauna sabon kwantiragi da tsohon mai tsaron raga a Arsenal daga Poland, Wojciech Szczesny mai shekara 34, cikin makonni masu zuwa. (Fabrizio Romano)
Arsenal da Liverpool na cikin ƙungiyoyin da suka matsa kaimi kan ɗan wasan Lyon da Belgium, Malick Fofana mai shekara 19, a lokacin bazarar nan. (CaughtOffside)










