Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa ƙuraje ke ɓata wa mata masu juna-biyu fuska?
- Marubuci, Adesola Ikulajolu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Aiko rahoto daga, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 4
"Idan na tuna baƙaƙen maganganun da mutane suka riƙa faɗa min game da ƙurajen, nakan yi kuka''.
Wannan shi ne halin da Chiamaka Okudoh - mace mai ƴaƴa uku - ke fuskanta saboda yadda fuskarta ke cika da ƙujare a duk lokacin da ta samu juna biyu.
Mata da dama kan fuskanci wannan matsala ta ƙurajen fuska - da wasu ke kira ''Bar-ni-da-mugu'' - inda a wasu lokutan take zama gagaruma.
Chiamaka ta ce a lokacin da ta fara ganin ƙurajen a fuskarta ba ta ɗauka wani abin damuwa ba ne, sai lokacin da ta je asibiti, sannan likita ya yi mata wasu gwaje-gwaje, daga nan ya ce tana da juna biyu, kuma shi ne dalilin waɗannan ƙurajen na fuskarta.
A wata hira ta musamman a sashen Pidgin na BBC ta bayyana wahalar da ƙurajen suka haifar mata da tsangwamar da ta fuskanta cikin jama'a.
"Idan na tuna irin abubuwan da mutane suka riƙa faɗa min, nakan yi kuka, saboda mutanen da suka kamata su tausayamin, su ke faɗa min maganganu na tsangwama,'' in ji ta.
Mene ne ƙurajen fuska?
Wata lalaura ce da fata kan fuskanta, a wasu lokutan sukan haifar da jin zafi idan an taɓa su. Sannan akwai ƙurajen da ke fitowa a fuskar masu juna-biyu da kuma wasu sassan jikinsu.
Yayin da ƙuraje suka zama ruwan dare tsakanin mata matasa musamman waɗanda suka kai shekarun balaga, wasu mazan ma kan fuskance ta a shekarun balagarsu.
Dakta Anjali Mahto, ƙwararriyar likitar fata ta shaida wa BBC cewa ba mayukan shafawa ne ke haddasa wa masu juna biyu ƙuraje ba, matsalar na faruwa ne sakamakon sauyin da jiki ya samu sakamakon shigar juna biyu.
Ta ƙara da cewa wani dalilin da ke ƙara haddasa ƙurajen shi ne ƙwayoyin halitta na gado, to amma ta ce matsalar na da magani.
Ƙurajen na da nau'ika daban-daban da ke fitowa mutane bisa dalilai mabambanta.
Nau'in da Chiamaka ta fuskanta shi ne manya-manya masu ɗigon baƙi a kansu, waɗan kuma suka cika mata fuska.
"Wasu lokuta sukan yi mini zafi idan na taɓa su,'' in ji ta.
Me ke haifar da ƙuraje a fata?
Hukumar Lafiya ta Birtaniya, NHS ta ce akwai nau'ikan ƙuraje da fitowa sakamakon ƙwayoyin halittar gado da waɗanda ake samu sakamakon wasu sauye-sauye a ƙwayoyin halitta musamman lokacin al'ada da juna-biyu.
Wani rahoton hukumar ya bayyana cewa babu wata hujja da ke nuna cewa rashin tsafta ne ke haifar da ƙurajen.
Hukumar NHS ta ce babu wani tasiri da tsaftace fata ke yi wajen kawar da waɗannan ƙuraje.
Chiamaka ta ce ta fara ganin ƙurajen ne a lokacin da ta samu juna-biyu, kuma likita ya tabbatar mata cewa za ta riƙa ganin wasu sauye-sauye masu yawa a jikinta.
"Likita ya buƙaci na yi gwaji, saboda a lokacin ban san abin da ya haifar min da ƙurajen ba, bayan na yi gwajin ne aka tabbatar ina ɗauke da juna-biyu, kuma ya ce shi ne dalilin ƙurajen nawa.''
Dakta Anjali ta ce mutane da yawa suna alaƙanta ƙurajen da cin abinci mai maiƙo da yawa, kuma akwai hujjar likitanci da ke cewa cin abincin da ke ƙara yawan siga a jii ne ke haifar da ƙurajen.
''Mutane sun ɗauka cewa cin abinci mai ɗauke da maiƙo da yawa ne ke haifar da ƙurajen. Amma hujjar likitanci ta nuna cewa cin abincin da ke ƙara yawan sinadarin siga a jiki ne ke haifar da ƙurajen. Irin waɗannan abinci na daga cikin abincin da aka fi son ci, amma kuma ba a so cinsu ya wuce ƙima''.
Magani da yadda za a kauce musu
Dakta Mahto ta ce wasu ƙurajen kan fito da baƙin kai wasu kuma da farin kai.
da fari sukan fiton ƙanana-ƙanana a kan fata, kuma sun fi fitowa a goshi da kumatu.
Wasu ƙurajen kan ɗuri farin ruwa ko mai launin ɗorawa a cikinsu.
Chiamaka ta ce ta riƙa shafa wani agani, kodayake ta ce bai yi mata aiki ba.
"Na fara ɗauar matakan kula da lafiya ta hanyar abincin da nake ci, na haƙura da gishiri da haƙura da askirim da Pizza da kuma boga. Na koma cin abinci mai ganyayyaki, da ƴaƴan itatuwa na haƙra da dun nau'ikan abincin masu ɗauke da maƙo''.
Amma dakta Mahto ta ce akwai magungunan da dama da ke taimaka wa wajen magance ko kawar da wadanann ƙuraje.
To sai dai ta shawarci mutane su kauce wa sayen magani ba tare da shwarar likita ba.
"Shawarata ita ce mutane su guje wa sayen magani da ka, saboda hakan ka iya haifar da wata matsalar da za ta iya zama gagaruma fiye da wadda ake ƙoƙarin magancewa'', in ji ta.
Ta ƙara da cewa yana da kyau a tuntuɓi likitan fata, musamman ga wadanda suke da juna-biyu ko masu shayarwa, domin sanin maganin ƙurajen da ya kamata ki sha.