Arsenal za ta raba gari da Partey, Manchester United na zawarcin Kean

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Thomas Partey zai bar Arsenal idan kwantiraginsa ya ƙare a farkon wannan makon bayan ɗan wasan Ghana mai shekara 32 ya kasa amincewa da sabuwar yarjejeniya da ƙungiyar ta arewacin Landan. (Athletic)

Manchester United na ci gaba da zawarcin ɗan wasan Fiorentina da Italiya Moise Kean mai shekara 25, mai shekara 25, wanda ke ɗauke da farashin fam miliyan 44, a ƙunshe a cikin kwantiraginsa. (Corriere dello Sport)

Arsenal na shirin hamayya da Chelsea da Liverpool, da kuma Manchester United wajen zawarcin ɗan wasan Eintracht Frankfurt ɗan kasar Faransa Hugo Ekitike mai shekara 23. (Sport Bild)

Borussia Dortmund da Bayer Leverkusen da Eintracht Frankfurt da RB Leipzig da kuma Stuttgart na cikin jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan tsakiyar Manchester City da Ingila James McAtee mai shekara 22 . (Times)

Liverpool a shirye take ta bayar da ɗan wasan Scotland Ben Doak mai shekara 19 a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da za ta ƙulla da Crystal Palace kan ɗan wasan baya na Ingila Marc Guehi mai shekara 24. (Sun)

Ɗan wasan Sporting ɗan ƙasar Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, ya shaida wa kulob ɗin cewa ba zai koma taka leda a ƙungiyar ba domin yana son ya sauya sheƙa a wannan bazarar. (Record)

Sunderland ta miƙa wa Reinildo Mandava kwantiragin shekara biyu kan albashin fam 65,000 kowanne mako bayan da Atletico Madrid ta sallami ɗan wasan bayan Mozambique mai shekara 31. (Guardian)

Nottingham Forest na daf da kammala cinikin ɗan wasan gaban Botafogo ɗan ƙasar Brazil Igor Jesus mai shekara 24 kan farashin fam miliyan 10. (Telegraph)

Manchester United a shirye ta ke ta rage farashin da ta ƙaƙabawaTyrell Malacia bayan PSV Eindhoven ta yanke shawarar ƙin amincewa da yarjejeniyar zaman dindindin da ɗan wasan na Netherlands mai shekara 25 bayan zaman aro da ya yi a ƙungiyar a kakar da ta gabata. (Mirror)

Sunderland na daga cikin ƙungiyoyin gasar Premier da dama da ke son ɗaukar ɗan wasan bayan Toulouse da Ingila ƴan ƙasa da shekara 21, Charlie Cresswell, mai shekara 22, wanda ke dafarashin fam miliyan 18 a kwantiraginsa. (Sun)

Qatar ta tattauna da Fifa kan yiwuwar karɓar baƙuncin gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi na shekarar 2029, wanda zai zame dole a gudanar a cikin hunturu. (Guardian)