Na fita daga APC ne saboda an zagi yayan Shugaba Buhari - Fatihu Muhammad

Bayanan bidiyo, Na fita daga APC ne saboda an zagi yayan Shugaba Buhari - Fatihu Muhammad
Na fita daga APC ne saboda an zagi yayan Shugaba Buhari - Fatihu Muhammad
An wallafa

Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Dan majalisar wakilan Najeriya da ke wakiltar mazabar Daura da Sandamu da Mai'adua, Fatihu Muhammad, ya ce ya fita daga jam'iyyar APC mai mulkin kasar ne saboda wani ya zazzagi mahaifinsa.

Fatihu Muhammad, ɗa ne ga yayan Shugaba Muhammadu Buhari.

A hirarsa da BBC, dan majalisar, wanda ya yi zargin cewa an murde zaben fitar da gwani na jam'iyyar domin bai wa wani damar yin takarar kujerar majalisar wakilan tarayya a zaben 2023, ya ce mutumin da aka bai wa takarar ne ya kirawo shi a waya ya zazzagi mahaifinsa.

"Idan kai dan halak ne aka ci mutuncin iyayenka, me ya kamata ka yi? In dai ka san darajar mahaifanka. Ai siyasa ba hauka ba ce," in ji shi.

Ya kara da cewa rashin adalci shi ne kashin bayan barinsa APC baya ga zagin mahaifinsa yana mai cewa jam'iyyar ta yi masa karfa-karfa a zaben fitar da gwani.

"Idan kana siyasa ka san yau za ka ci, gobe ba za ka ci ba: adon siyasa ke nan. A yi zabe, idan Allah ya bai ba ni nasara ba zan rungumi kaddara, na gyara kura-kuraina na tunkari gaba, amma sai a ce wai za a karya ka," in ji Honorabul Fatihu.

Dan majalisar wakilan na Najeriya ya ttabbatar da cewa ya gana da dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar da zummar sauya sheka, yana mai cewa bai gaya wa Shugaba Buhari abin da ya faru da shi ba.