Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dakatar da Sarkin da ya naɗa 'ƙasurgumin ɗan fashi' sarauta a Zamfara
Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta dakatar da Sarkin 'Yandoton Daji bayan da ya bai wa wani jagoran 'yan fashin daji, Adamu Aliero, sarautar Sarkin Fulani.
Gwamnatin ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar wadda ta samu sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Kabiru Balarabe Sardauna, tun farko gwamnatin ba ta da masaniyar naɗin da aka yi wa Adamu, wanda hukumomi ke nema ruwa-a-jallo.
Sanarwar ta ce a yanzu an mika riƙon sarkin garin na 'Yandoto ga Alhaji Mahe Garba Marafa, wanda shi ne Hakimin 'Yandoto.
Haka nan sanarwar ta ce gwamnati ta kafa kwamitin da zai yi bincike kan naɗin sarautar da aka yi wa mutumin da ake kira Ado Aliero.
A ranar Asabar ne dai bayanai suka fito kan yadda Sarkin na 'Yandoto ya naɗa Adamu Alieru 'Yankuzo, wanda ake zargin jagoran 'yan fashin daji ne a matsayin Sarkin Fulani, lamarin da ya janyo suka daga bangarori da dama.
Dama an dade ana zargin wasu sarakuna da taimaka wa ‘yan fashin daji wurin aiwatar da ta’asar da suke yi, inda aka sauke wasu daga kan mukamansu.
'Har yanzu muna neman Adamu Aliero’
A cewar rundunar 'yan-sandan Najeriya, ta bayar da cigiyar wanda aka naɗa sarautar ne shekaru biyu da suka gabata.
SP Gambo Isa, wanda shi ne mai magana da yawun rundunar 'yan-sandan Najeriya a jihar Katsina, ya tabbatar wa BBC da batun.
Ya ce "Adamu Aliero na daga cikin masu kashe mutane da kama mutane su yi garkuwa da su, kuma muna nemansa a kan aikin ta'addanci da ya yi a garin Kadisau, inda ya kashe sama da mutum ɗari."
Ya ƙara da cewa "Mun yi gangami tare da 'yan-jarida da tsohon Kwamishinan 'yan-sanda Sunusi Buba, muka je garin Kadisau muka ga kisan-gilla da ya yi wa mutane."
Wannan ne ya sa rundunar 'yan-sanda reshen jihar Katsina ta fitar da sanarwar cewar duk wanda ya kawo Adamu Aliero a raye za a ba shi (ladan) Naira miliyan biyar, kuma maganar tana nan.
Neman shi muke yi, duk wanda ya gan shi ya kamo shi, ya kawo mana shi saboda ana zargin shi da kisan gilla kan mutanen Kadisau. Ba ma Kadisau kaɗai ba akwai sauran garuruwa da al'umma da ya sata ya karbi kuɗin fansa"
Wasu mutanen 'Yandoto sun yi murna da naɗin da aka yi wa Adamu Alieru
Sai dai wani lamari shi ne yadda wani mutumin 'Yandoto da BBC ta zanta da shi ya ce wasu al'ummar yankin sun yi murna da naɗin da aka yi wa wanda ake zargin ɗan fashin dajin ne.
Ya ce "Abin ya ƙayatar da ni, kuma na yi farin ciki sosai."
Lokacin da BBC ta tambaye shi me ya sa yake farin ciki duk da wasu na ganin naɗin bai dace ba?
Sai ya ce "Mu da muke a wannan yanki muna tunanin wannan bawan Allah yana son zaman lafiya domin da alama ya bar abin da yake yi."
Ya ƙara da cewa "Rabon da a koro mu daga daji har mun manta, mun samu natsuwa wallahi."
"A baya suna koro mutane kafin a yi sasanci, amma bayan an yi sasanci, da kuma wannan naɗin sarauta da aka mashi, za ka je daji sai ka yi zufa (ka gaji) kafin ka dawo gida. Kuma muna fatan Allah shi ba mu zaman lafiya sanadiyyar wannan naɗi."
Mece ce makomar sarautar da aka bai wa Ado Alieru?
Sanarwar da gwamnatin jihar Zamfarar ta fitar ba ta fayyace makomar sarautar da aka bai wa wanda ake zargin sa da zama ɗan fashin dajin ba.
Haka nan kuma ba ta fayyace makomarsa, shi kansa ba.
Ana dai zargin sa ne da jagorantar kai wani mummunan hari da ya yi sanadiyyar kashe sama da mutum 50 a cikin shekara ta 2020, a jihar Katsina da ke maƙwaftaka da jihar ta Zamfara.
Tun daga wancan lokaci ne rundunar 'yansanda ta Najeriya ta bayar da cigiyar sa, sai dai har yanzu ba a kama shi ba.