'Mun kwashe sati biyu muna kokarin hana ambaliyar ruwa cin kauyenmu a Jigawa'

Bayanan bidiyo, Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
'Mun kwashe sati biyu muna kokarin hana ambaliyar ruwa cin kauyenmu a Jigawa'
An wallafa

Wasu a'ummar Jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya sun bayyana yadda mamakon ruwan saman da ake yi ya lalata gine-ginensu.

Sun bayyana wa BBC Hausa cewa tun da matsalar ambaliyar ruwan ta soma ba sa iya barci da idanunsu biyu.

Wasu al'ummar kauyen Majiyawa da ke karamar hukumar Ringim sun gaya mana cewa lamarin ya fi karfinsu.

Malam Tijjani Yakubu, wani dattijo a kauyen na Majiyawa, ya ce "Ruwan kogi ne yanzu ya addabe mu, saboda mun nemi taimakon buhunhuna an taimaka mana amma abin ya fi karfinmu.

Ba dare ba rana wajen satin mu biyu muna fama da wannan aiki."