Gane Mini Hanya: Muhimmancin adabi ga rayuwar al'umma

Bayanan sautiLatsa sama don sauraron shirin
Gane Mini Hanya: Muhimmancin adabi ga rayuwar al'umma
An wallafa

Masana harshen al’ada sun bayyana irin muhimmancin da adabi ke da shi ta fuskoki da dama wajen ginin rayuwar al’umma.

Adabi ya zama wani tubali da kowace al’umma ke tinkaho da shi da zai taimaka masu sanin inda suke, da kuma inda suka dosa.

A shekarar 1933 Turawan mulki mallaka a Najeriya, karkashin jagorancin Rupert East, sun kirkiro wata gasa da ta kai ga samar da littatafan adabi na farko a harshen Hausa da suka haɗa da Ruwan Bagaja da Gandoki da Shehu Umar da sauran su.

Duk da yake ba su ne littatafan Hausa na farko da aka fara samarwa ba, amma dai sun zama harsashin yaɗuwar rubutaccen adabi a harshen tun daga wancan lokaci.

Daga baya an samu sauye-sauye da suka kai ga raguwar karance-karance tsakanin al’umma, abin da ake kallo da babban koma baya a fannin na adabi.

Filin mu na Gane Mini hanya na wannan makon, Zubairu Ahmad ya yi hira da Farfesa Bello Daudun Bada, malami a Sashen Nazarin Harshen Ingilishi da Adabi na Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, wanda ya yi karin bayani kan muhimmancin adabi da kuma irin kalubalen da yake fuskanta a yanzu.