BBC ta bankado yadda manyan kamfanonin turaren alfarma ke da hannu wajen bautar da yara

Basmalla a gonar furannin jasmine
Bayanan hoto, Basmalla ƴar shekara10 da y'an uwanta suna tsintar furen jasmine da daddare don taimakawa mahaifiyarsu ta samu biyan buƙata
    • Marubuci, Ahmed ElShamy and Natasha Cox
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Eye Investigations
  • An wallafa

Wani binciken BBC ya gano cewa ana sanya yara aiki mai wahala ta hanyar tsintar kayan haɗi da wasu manyan kamfanoni kayan kwalliya biyu ke amfani da su.

Binciken kan hanyoyin samar da turare a lokacin bazara ya nuna cewa yara ƙanana suna tsintar furen jasmine da kamfanonin kayan kwalliya na Lancôme da Aerin Beauty ke amfani da su wajen yin turare.

Duk da iƙirarin da manyan kamfanonin haɗa turare suke yi na cewa ba za su taɓa saka yara aiki ba, binciken BBC ya ƙalubalanci waɗannan ikirari.

Babban kamfanin kayan kwalliya na L'Oréal, wanda ya mallaki Lancôme, ya tabbatar da sadaukarwar sa na kare hakkin dan’adam, yayin da Estée Lauder, iyayen kamfanin Aerin Beauty, ya ce ya tuntuɓi masu samar musu da kayan haɗi.

Furen Jasmine da ake amfani da shi a wajen haɗa turaren Lancôme Idôle L'Intense da Aerin Beauty's Ikat Jasmine da Limone Di Sicilia ta samo asali ne daga Masar, wanda ke samar da kisan rabin furanni jasmine na duniya, wani muhimmin kayan haɗa turare.

Masu binciken masana'antu sun bayyana cewa manyan kamfanonin da ke samar da kayayyakin alatu da dama suna yanke kasafin kudi, wanda ke haifar da karancin albashi.

Wannan matsalar kuɗi ta tilasta wa masu tsinkar furen jasmine na Masar suna bautar da 'ya'yansu wajen tsinkar furanni

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bugu da ƙari, binciken ya fallasa manyan kurakurai a cikin tsarin tantance hanyar samar da kayan kamshi na masana'antar turare.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan ayyukan bautar da ake yi a wannan zamani, Tomoya Obokata, ya bayyana damuwarsa kan hujjojin da BBC ta bayar, wadanda suka hada da faifan video da aka ɗauka a ɓoye daga gonakin furen jasmine na Masar a lokacin girbin bara.

"A takarda, masana'antar ta yi alkawarin samar da gaskiya da kuma yaki da bautar da yara. Amma wannan faifan ya nuna sun kasa cika wadannan alkawurran," in ji Obokata.

Heba, mazaunin wani kauye a Gharbia, wani yankin na Masar tana tusa ƙeyar ƴaƴantatun daga ƙarfe 03:00 na safe domin tsinkar furanni kafin rana ta lalata su.

Ta dogara ga 'ya'yanta hudu, masu shekaru 5 zuwa 15, wajen taimaka mata.

Kamar mafi yawan mutanen da ke tsinkar furen jasmine a Masar, Heba ta kasance tana aiki ita kaɗai mai zaman kanta” da ke aiki a wata ƙaramar gona. Abin da take samu ya dogara ne akan furanni nawa ita da 'ya'yanta suka tsinta.

A daren da BBC ta dauki fim din ta, Heba da 'ya'yanta sun tsinka furannin jasmine kilo 1.5 a gonar furannin jasmine. Bayan ta ba da kashi uku na abin da ta samu ga mai gidan ko gonar, kusan kuɗi dala 1.50 ne ya rage mata a aikin da tayi.

Sakamakon hauhawar hauhawar farashin kayayyaki a Masar, wannan adadin ba zai mata komai ba kuma da yawa daga cikin masu tsinkar furen suna rayuwa ne ƙasa da kangin talauci.

Heba tana tsinkar jasmine da fitilar kai
Bayanan hoto, Iyalin Heba suna anfani da fitila guda ɗaya don ƙoƙarin ganin abin da suke yi yayin tsinkar furen jasmine da dare.

‘Yar Heba ‘yar shekara 10 mai suna Basmalla ta kamu da rashin lafiyar ido. A lokacin shawarwarin likita da muka halarta, likitan ya yi gargadin cewa zai iya shafar ganinta idan ta ci gaba da tsinkar furen jasmine ba tare da magance kumburin ba.

Da zarar an tsinki furen jasmine ɗin tare da kuma auna shi, sai a tura shi ta wuraren tattarawa zuwa ɗaya daga cikin masana'antun gida da yawa waɗanda ke hako mai daga furannin. Manyan masana'antu uku sun haɗa da A Fakhry and Co, Hashem Brothers, da Machalico.

Kowace shekara, waɗannan masana'antun suna saita farashin furen jasmine da ma'aikata kamar Heba ke tsinkowa

Yana da wuya a tantance ainihin adadin yara a cikin mutum 30,000 da ke da hannu a masana'antar jasmine ta Masar.

Amma kuma a lokacin bazara na 2023, BBC ta yi fim a duk faɗin wannan yanki kuma ta yi magana da mazauna da yawa inda suka ba da rahoton cewa ƙarancin farashin furen jasmine ne ya saka su bautar da yaran su cikin aikin.

Yawan yaran da ke girbin turare a Gharbia, Masar
Bayanan hoto, Yara da BBC ta gani suna tsinkar jasmine domin yin turare

Mun lura da cewa a wurare hudu daban-daban, ɗimbin masu aikin tsinkar furen jasmine a gonakin da ke samar wa da manyan masana'antu yara ne 'yan ƙasa da shekaru 15.

Hakazalika majiyoyi da yawa sun shaida mana cewa yara suna aiki a gonakin da masana'antar Machalico ta mallaka kai tsaye. Domin tabbatar da hakan, mun bi ta ƙrƙashin ƙasa domin gano masu tsinkar furen wadanda suka bayyana mana shekarun su tsakanin 12 zuwa 14.

Haramun ne a Masar ga duk wanda bai kai shekara 15 ba ya yi aiki tsakanin sa'o'i 19:00 zuwa 07:00.

Kamfanonin na fitar da man jasmine zuwa gidajen kamshi na duniya, inda ake samar da turare. Ɗaya daga cikin manyan gidajen kamshi shine Givaudan, wanda ke zaune a Switzerland, wanda ke da dangantaka mai tsawo da A Fakhry da Co.

Wani yaro da muka hadu da shi a lokacin daukar a boye a wata gona mallakar masana'antar turare ta Machalico
Bayanan hoto, Wani yaro da muka hadu da shi a lokacin daukar a boye a wata gona mallakar masana'antar turare ta Machalico

Duk da haka, manyan kamfanonin turare, irin su L'Oréal da Estée Lauder ne ke riƙe da dukkan iko, a cewar wani mai turare da ke zaman kansa Christophe Laudamiel da wasu masana'antu da dama. Kamfanonin da aka fi sani da "jagorori," suna saita taƙaitacciyar kasafin kuɗi ga gidajen ƙamshi.

Mista Laudamiel, wanda ya kwashe shekaru yana aiki a cikin daya daga cikin gidajen kamshin ya ce, "Sha'awar jagororin ita ce a samu man furen jasmine mafi arha da za a iya sakawa a cikin kwalbar kamshin sannan kuma a sayar da shi a farashi mafi girma."

Ya bayyana cewa, duk da cewa wadannan kamfanoni ba sa kula da albashin masu girbin furen kai tsaye ko kuma farashin jasmine, tsananin kasafin kudin da suke da shi yana haifar da matsin lamba mai rikitarwa ga masana’antu da kuma masu tsinkar furen.

"Akwai babban bambanci tsakanin abubuwan masu tallace-tallacen turaren suke cewa da kuma abin da a zahiri ake bai wa masu girbin furen," in ji shi.

Christophe Laudamiel, mai turare da ke zaman kansa
Bayanan hoto, Christophe Laudamiel yace ana murɗe kasafin kudi

A cikin kayan tallan su, kamfanonin turare da gidajen kamshi suna tabbatar da yin ayyuka ta hanyar da'a. Kowane ma'aikaci a cikin hanyar samar da kayayyaki ya sanya hannu kan wasiƙar sadaukarwa ga Majalisar Dinkin Duniya, tare da yin alƙawarin bin ƙa'idodinta game da ayyukan aiki masu aminci da kawar da ayyukan bautar da yara.

Koyaya, wani babban jami'in gidan kamshi na Givaudan, wanda ke magana ba tare da sunansa ba, ya bayyana wani muhimmin batu: kamfanonin turaren ba su da sa ido sosai kan hanyoyin samar da kayayyaki.

Waɗannan kamfanoni sun dogara da gidajen ƙamshi wajen hayar kamfanonin tantancewa don tabbatar da ƙwazo.

Kamfanonin tantancewa da aka fi yawan ambata ta hanyar haɗin gwiwa da gidajen kamshi sune Sedex da UEBT. Duk da yake ba a iya samun rahoton binciken su a bainar jama'a, mun sami nasarar samun su daga masana'antar A Fakhry and Co ta hanyar.

Rahoton UEBT, dangane da ziyarar masana'anta a bara, ya nuna batun haƙƙin ɗan adam amma bai bayar da cikakkun bayanai ba. Duk da wannan, kamfanin ya sami "tabbaci," yana ba shi damar yin iƙirarin cewa yana ba da "man jasmine da aka samo asali."

UEBT, a cikin martanin da ta mayar kan wannan, ta ce: "An ba da kamfani ɗaya da alhakin samar da shaida, ƙarƙashin tsarin aiki wanda zai yi aiki har zuwa tsakiyar 2024, kuma za a janye idan ba a aiwatar da shi ba."

Sarah Dadush, Lauya ce wacce ta kafa wani shiri wanda ke neman inganta hakin bil'adama a cikin hanyar samar da kayayyaki a duniya, ta ce binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewa wadannan tsarin ba sa aiki.

Batun, in ji ta, shi ne, "masu binciken na duban abin da aka biya su ne kawai don tantancewa", kuma wannan ba zai hada da farashin da ake biyan ma'aikata ba - "babban dalilin" aikin bautar da yara.

Wani Fakhry da Co sun gaya mana cewa an haramta yin aikin yara a gonakinsu da masana'anta, amma yawancin furen jasmine da suke amfani da shi na samo asali ne daga masu tsinkowa da ke zaman kansu.

"A cikin 2018, a karkashin kulawar UEBT, mun fara aikin Rage Kayayyakin tsirrai na furen Jasmine, wanda ya haramtawa mutane 'yan kasa da shekaru 18 aiki a gonaki."

Kamfanin Machalico ya ce ba ya amfani yara ƙasa da shekara 18 wajen aikin tsinkar furen jasmine kuma ya ce ya kara farashin furen jasmine a shekaru biyu da suka gabata, kuma za ya sake yin hakan a bana. Hashem Brothers ya ce rahoton namu ya ta'allaka ne kan bayanan da ba su dace ba.

Basmalla a kan hanyar ta zuwa ganin likitan ido kan ciwon idon da ta samu
Bayanan hoto, Basmalla a kan hanyar ta zuwa ganin likitan ido kan ciwon idon da ta samu

Givaudan, gidan yin turare da ke yin turaren Lancôme Idôle L'Intense, ya bayyana bincikenmu a matsayin "mai matukar tayar da hankali", yana mai karawa da cewa "ya zama wajibi a kanmu duka mu ci gaba da daukar matakin kawar da kasadar yin aiki ta hanyar bauytar da yara gaba daya".

Firmenich, gidan turaren wanda ke yin Ikat Jasmine da Limone Di Sicilia don Aerin Beauty, a lokacin rani a shekarar 2023 ya samo furen jasmine daga kamfanin Machalico, ya gaya mana cewa yanzu yana amfani da sabon mai siyar da jasmine a Masar.

Ta kara da cewa "zata tallafawa shirye-shiryen da ke neman magance wannan matsala tare da abokan aikin masana'antu da manoman jasmine na gida".

Mun kuma miƙa sakamakon binciken ga jagororin masu yin turare.

Kamfanin L'Oréal ya ce "ya himmatu sosai wajen mutunta ka'idojin kare hakkin bil'adama da aka amince da su a duniya", ya kara da cewa "ba ya taba neman gidajen yin turare da su yi kasa da farashin kayan masarufi a kan manoma ba.

Kamfanin Estée Lauder ya ce: "Mun yi imanin cewa ya kamata a kiyaye haƙƙin dukan yara. Kuma mun tuntuɓi masu samar da mu kayan aiki don bincikar wannan matsalar mai tsanani. Mun fahimci yanayin zamantakewa da tattalin arziki mai rikitarwa da ke tattare da tsarin samar da jasmine na gida, kuma muna daukar mataki don magance matsalar."

A Gharbia, Heba mai tsinkar furen jasmine ta yi mamaki lokacin da muka gaya mata farashin yadda ake sayar da turaren jasmine a kasuwannin duniya.

"Ba a daraja mutane a nan," in ji ta.

"Ban damu da mutane suna amfani da turare ba, amma ina son masu amfani da wannan turaren su ga raɗaɗin halin da yara ke cikin. Kuma su yi magana."

Sai dai lauya Sarah Dadush ta ce alhakin bai rataya kan mabukaci ba kaɗai ba.

"Wannan ba matsala ba ce da ya kamata mu magance. Muna buƙatar doka, muna buƙatar bayanin kamfanoni kan abubuwan da suka gudanarwa, kuma hakan ba zai iya kasancewa kan masu amfani kawai ba."