Bayern Munich ta dakatar da Mane kan naushin Sane

An wallafa

Bayern Munich ta ajiye Sadio Mane a wasan da za ta kara da Hoffenheim ranar Asabar, sakamakon naushin Leroy Sane da ake zarginsa.

Ranar Asabar Bayern za ta karbi bakuncin Hoffeinheim a wasan mako na 28 a gasar Bundesliga.

Wasu rahotanni daga Jamus na tuhumar Mane da naushin Sane, bayan tashi daga Champions League ranar Talata da Manchester City ta ci 3-0 a Etihad.

An ce sai da 'yan wasa suka shiga tsakanin Mane da Sane kan bai wa hammata iska da suka yi a dakin hutun 'yan kwallo.

Bayern ta sanar cewar ta dakatar da dan kwallon Senegal saboda nuna hali na rashin kyautawa, ta kuma ce za ta ci tarar dan wasan.

Bild ta ruwaito cewar tsohon dan wasan Liverpool, Mane, gwarzon dan kwallon Afirka karo biyu, ya yi korafi kan kalaman da Sane yake masa, saboda rashin nasarar bayan tashi a Etihad.

Bayan da suka koma Jamus aka dauki Mane a mota shi kadai a filin sauka da tashin jirgi, shi kuwa Sane ya shiga bas tare da 'yan wasa zuwa sansannin Bayern Munich.

Har yanzu ba a ji ta bakin Mane ko Sane ba kan lamarin da ya faru.

Bayern za ta karbi bakuncin City a wasa na biyu zagayen quarter finals a Jamus ranar Laraba.