Cututtuka biyar da rashin bishiya ke haddasawa

Cututtuka biyar da rashin bishiya ke haddasawa
An wallafa

Dr Hashim Muhammad Dahiru, wani likita ne a Najeriya da ya mayar da hankalinsa ga samar da ingantaccen muhalli.

Ta hanyar gidauniyarsa mai suna Panacea Foundation, Dr Dahiru ya dasa bishiyoyi fiye da dubu 100 a fadin jihar Kano.

"Burina shi ne samar da muhallin da zai zama mai inganci ga dan adam", in ji Dr Dahiru.

Likitan ya lissafa wasu cutuka guda biyar da ya ce rashin bishiya a muhalli na haddasu.