Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An tashi 1-1 tsakanin Leipzig da Man City a Jamus
Manchester City ta tashi 1-1 da RB Leipzig a wasan farko a Champions League zagayen 'yan 16 da suka kara a Jamusu ranar Laraba.
Minti na 27 da take Leda City ta ci kwallo ta hannun Riyad Mahrez, yayin da Leipzig ta farke ta hannun 'Josko Gvardiol a minti na 70.
Ranar 14 ga watan Maris City za ta karbi bakuncin Leipzig a wasa na biyu, domin neman gurbin zuwa quarter finals.
City ta kawo wannan gurbin bayan da ta yi ta daya a rukuni na bakwai da maki 14, Leipzig kuwa ta hada maki 12 ta yi ta biyu a rukuni na shida.
Sun kara a kakar bara a Champions League, City ta ci 6-3 a Etihad a Satumba, Leipzig ta yi nasara 2-1 a Disambar 2021.
Ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu City wadda take ta biyu a teburin Premier za ta ziyarci Bournemouth a wasan mako na 25.
Wasa da aka buga tsakanin Leipzig da Man City:
2022/23 Champions League
RB Leipzig 1-1. Man City
2021/2022 Champions League
- RB Leipzig 2 - 1 Man City
Champions League
- Man City 6 - 3 RB Leipzig