Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya
Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta nuna damuwa kan matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a Najeriya.
Kungiyar ta bukaci mahukuntam kasar da su gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu wahalhalu da suke fama da su.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin mai alfarma sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ta ce abin damuwa ne kan yadda wasu al'umma suka fara zanga-zanga sakamakon mawuyacin halin da suke ciki.
Ta ce yadda mutane suka fara harzuƙa na nuna cewa tura ta kai bango, kuma ishara ce ga mahukunta su ɗauki matakin gaggawa domin gudun kada al'ammura su gagari kundila.
Ta bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu raɗaɗi.
Haka ma Majalisar malamai da limamai a jihar Kaduna a yayin wani taron manema labarai da ta kira, ta ce mawuyacin halin da al’umma ke ciki ba zai misaltu ba.
Mamba na majalisar malaman Sheikh Idris Muhammad Sabongari ya ce abin ba dadi, babu yadda za a iya kwatanta halin da al'umma ke ciki, domin duk inda ake zaton lamarin to ya wuce nan
"A jiya naga wasu bayin Allah ganye suke ci nan cikin gari kenan, idan ka tafi karkara kusan kowa yadda kasan ciwon Aids ya kamasu duk sun rame, ana cewa matsala ce ta duniya amman mu matsalar ta fi ƙamari a Najeriya."
Majalisar malaman ta ce al'ummar Najeriya sun galabaita ne sakamakon janye tallafin man fetur. Ƙungiyar ta ce ƴan kasuwa ma na da alhakin halin da ake ciki.
Sheikh Aminu Umda mamba ne a majalisar ya kuma shaida wa BBC cewa gwamnati ita ce uba amma tare da dora laifi ga yankasuwa.
"Su ma ƴankasuwar za iya samun laifinsu, saboda yadda suke ƙarawa kayan masarufi kuɗi, za ka sawo kaya yau gobe ka koma ka ji an sauya farashinsa, talakawa na rayuwa cikin tsanani a ƙasar nan."
Duk da cewa an sha fuskantar matsalar tashin farashi a Najeriya, sai dai majalisar Malaman ta ce wannan karon lamarin ya sha bam-bam da irin wana aka fuskanta a baya.
"Rayuwar al'umma gaba ɗaya ta dogara kan man fetur, saboda haka kamata ya yi a ce gwamnati ta yi wani tsari mai kyau wanda mutane za su samu sauƙi kafin ta janye tallafin man fetur," in ji Sheikh Idris Muhammad Sabon gari.
Majalisar malaman ta ce addua ce mafita, ta kuma yi kira ga mahukunta da su ƙara ƙaimi wajen inganta matakan tsaro, wanda ya kawo cikas ga noma ga al'ummar arewacin ƙasar.
Najeriya dai na fama da hare-haren ƴanbindiga da kuma hauhauwar farashi, lamarin da ya fara tunzura ƴan ƙasar wajen yi wa hukumomin ƙasar bore.
Gwamnatin ƙasar ta fitar da wasu tsare-tsaren tallafin rage radadin janye tallafin man fetur, sai dai wasu da dama naganin ya kamata a sake yi wa tsare-tsaren garanbawul.