Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Sheikh Abubakar Muhammad Jibril, limamin masallacin BUK
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Sheikh Abubakar Muhammad Jibril ɗan asalin aka haife shi a Accra da ke Ghana cikin shekarar 1938.
A tattaunawarsa da BBC Hausa, malamin ya ce ya tashi a Accra inda galibin karatun da ya yi na addini ne.
Ya yi faɗi-tashin karatu kafin ya soma aiki tare da ofishin jakadancin Saudiyya, daga nan ne kuma ya samu tallafin karatu zuwa ƙasar.
Ya yi karatu ƙarƙashin malamai kamar Sheikh Abdulazeez Ibn Baz da Muhammadul Amin al-Shinqiti da Malam Muhammad al-Mukhtar.
Malamin ya ce abin da ya fi faranta masa rai shi ne rayuwarsa a Madina. "Kodayaushe na tuna na yi salloli a masallacin Manzon Allah SAW, ina matuƙar jin dadi."
Ya ci gaba da cewa: "Waɗannan manyan malamai da a lokacin a duniya babu kamarsu, ina jin daɗin kasancewar su ne malaman da suka karantar da ni."
Ya ce ya ɗauki salon huɗubar limamin da ke sallah a masallacin Annabi S.A.W., Abdulazeez Bn Saleh, "wanda a wannan lokacin babu limami kamarsa".
Sheikh Abubakar Muhammad Jibril ya ce a lokacin da ya tafi Saudiyya a 1965, ba shi da aure, kafin ya je hutu bayan shekara biyar.
"Da na je hutu sai iyaye suka fara tunanin bai kamata na koma babu mata ba" sai aka hada ni da iyali kuma sun haifi yarinya ɗaya daga baya kuma suka sami ɗa namiji.
Ya ce bayan matarsa ta farko ta rasu, ya sake wani auren inda suka haifi yara huɗu.
Sheikh Abubakar Muhammad Jibril ya ce rayuwar da iyaye suka yi akwai zumunci da girmama manya. "Wancan lokacin har siyasa da aka yi, ba irinta ake yi yanzu ba.
"Su manya da suka tashi suna neman haƙƙi na ƙasashensu, nema suke da gaske, al'amarin yanzu ba haka yake ba, babu daɗi", a cewarsa.
Ya ce taɓarɓarewar tsaro da ake gani a Najeriya na faruwa ne saboda an saki hanyoyin Ubangiji, "da an bi tarbiya, da al'amari bai zama haka ba."