Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Haaland ya ci kwallo na tara a Premier League
Manchester City ta doke Brighton 2-1 a wasan mako na tara a Premier League da suka buga ranar Asabar a Etihad.
Tun kafin wannan makon, City ta yi rashin nasara a wasa biyu a babbar gasar tamaula ta Ingila, bayan da Wolverhampton da Arsenal suka doke ta.
Hakan ne ya sa kungiyar Etihad ta saka kaimi ta fara cin kwallo ta hannun Julian Alvarez, daga baya Erling Haaaland ya kara na biyu.
Haaland wanda ya zira kwallo na tara a gasar Premier ta bana, ya kawo karshen wasa ukun da ya yi ba tare da cin kwallo ba.
Bayan da suka koma zagaye na biyu, Brigton ta kara sa kaimi, har ma Ansu Fati ya farke mata kwallo ɗaya a minti na 73.
Doku ya taka rawar gani daga bangaren hagu daga gaba, wanda shi ne ya bai wa Alvarez kwallon da ya ci Brighton.
Dan wasan tawagar Argentina, Alvarez kadan ya rage ya kara cin kwallo a fafatawar, bayan wani bugun tazara da ya yi.
Da wannan sakamakon City ta koma mataki na daya a teburin Premier, kafin Arsenal ta tashi wasan da ta je Chelsea a Stamford Bridge ranar Asabar.