Man United ta sayi Mount

An wallafa

Manchester United da Chelsea sun cimma matsaya kan sayen ɗan wasan tsakiya na Chelsea, Mason Mount kan kuɗi fan miliyan 55 da ɗoriya.

Mount zai sanya hannu da United ne kan kwantaragin zama na shekara biyar.

Ɗan wasan, mai shekara 24 shi ne na farko da koci Erik ten Hag ya siya tun bayan buɗe kasuwar musayar ƴan wasa.

Shi dai Mount ya je Chelsea ne tun yana ɗan shekara shida.

Chelsea na kokarin rage yawan 'yan kwallonta kuma tuni ta sayar da golanta Edouard Mendy da dan wasan baya Kalidou Koulibaly da kuma Mateo Kovacic.

Shi kuma Kante ya bar Chelsea ya koma Al-Ittihad a yayin da Ruben Loftus-Cheek yake gab da koma wa AC Milan.

Tiemoue Bakayoko shi ma ya bar Chelsea.