Camavinga zai yi jinya na ɗan wani lokaci

Camavinga

Asalin hoton, BBC Sport

An wallafa

Ɗan wasan Real Madrid Eduardo Camavinga ya samu rauni a gwiwarsa a lokacin da yake taka leda a Faransa.

Ɗan wasan mai shekaru 21 ya ji rauni a gwiwarsa ta dama a atisaye ranar Laraba, bayan da suka yi karo da ɗan wasan gaba Ousmane Dembele.

Sanarwar da kulob ɗin na La Liga ya fitar, ya ce Camavinga, wanda ya taka leda a kowane wasa a kakar bana, ya sami rauni a jijiyoyin gwiwarsa.

Ba a ba da lokacin da zai dawo ba.

Matsalar raunin 'yan wasan Carlo Ancelotti na ci gaba da ƙaruwa, yayin da Camavinga ya zama ɗan wasa na huɗu na Real da ya yi jinyar rauni a gwiwarsa.

A ranar Alhamis kuma, ɗan wasan gaban ƙungiyar Vinicius Jr ya fice saboda rauni a cinyarsa a wasan da Columbia ta doke Brazil da ci 2-1.

Mai tsaron gida Thibaut Courtois da ɗan wasan baya Eder Militao ba sun daɗe suna jinya bayan da aka yi musu tiyata.

Ɗan wasan gefe Arda Guler, wanda ya ƙulla yarjejeniya da Real a bazara, har yanzu bai buga wasansa na farko ba saboda rauni a gwiwarsa.