Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hugo Lloris ya aika sako na rarrashin Harry Kane
Kyaftin din Faranssa, Hugo Lloris ya ce ya aika sako na rarrashin kyaftin din Ingila, Harry Kane, bayan da suka fitar da su daga Gasar Kofin Duniya a Qatar.
Lloris ya ce da farko ya rasa kalaman da zai rubuta don rarrashin Kane, bayan da Faransa ta fitar da Ingila a wasan daf da na kusa da na karshe a wasan na Qatar.
Kane ya barar da fenariti da ya buga wa Lloris, inda Faransa ta yi nasarar kai wa zagayen daf da karshe da ci 2-1.
Ranar 26 ga watan Disamba, Lloris zai buga wa Tottenham wasan Premier League tare da Kane a fafatawa da Brentford.
''Wannan lokaci ne mai wahala da tawagar Ingila da shi kansa Harry Kane,'' Lloris.
''Na tura masa sako ana tashi daga wasan. Ba abu ne mai sauki ba ka hada kalaman da suka da ce don yin rarrashin. Yana bukatar hutu.
''Ina jin ya kamata ya yi alfahari da abubuwan da ya yi wa Ingila a wasannin da ke buga mata.
''A tarihin kwallon kafa, manyan fitattun 'yan wasa sun barar da fenati a tarihinsu na tamaula - kamar Lionel Messi da Cristiano Ronaldo - na kwan da sanin cewar Kane zai ci gaba da daga darajar Tottenham da kuma Ingila.''
Lloris, golan Faransa zai fuskanci Morocco a wasan daf da karshe a Gasar Cin Kofin Duniya ranar Laraba.
Faransa ce mai rike da kofin, wanda ta lashe a Rasha a 2018.