Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wace shekara ta fi dacewa yaro ya shiga jami'a?
Shekarun karatun yara batu ne da ya haifar da cecekuce a Najeriya, musamman ma shekarun soma karatun Jami'a.
Gwamnatin tarayya ta ce sai yaron da ya kai shekara 18 ko fiye ya cancanci shiga jami'a, kamar yadda aka ruwaito ministan ilimin ƙasar ya sanar a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
Kodayake akwai saɓani da aka samu a wajen taron wanda hukumar shirya jarabawar shiga Jami'a (JAMB) ta jagoranta inda wani ɓangaren na masu ruwa da tsaki a taron suka bayar da shawarar shekara 16 maimakon 18.
Suna ganin bai dace da a ce yaro ɗan shekara 16 ya ci jarabawar kammala sakandare (WAEC ko NECO) da kuma ta shiga Jami'a (JAMB) kuma a hana shi shiga Jami'a ba, matakin da daga baya aka ruwaito ministan Ilimin ƙasar Farfesa Tahir Mamman ya amince.
Hakan na nufin a hukumance an ƙayyade shekara 16 a matsayin shekarun shiga Jami'a a Najeriya.
Najeriya ƙasa ce da ke da tsarin karatu tun daga matakin firamare har zuwa shiga jami'a. Shekarun soma karatun yaro za su iya tantance shekarun kammala karatunsa musamman har zuwa lokacin da zai shiga Jami'a
Amma saboda wasu dalilai - akwai yara da dama da ake samu da ke ƙoƙarin shiga Jami'a, yayin da kuma shekarunsu ba su kai ba. Ko ya tsarin yake da matakin karatun yara a kasar?
Tsarin matakan shekarun karatu na yara
Najeriya na da tsarin matakai na karatun yara, kuma an dade ƙasar na amfani da tsarin.
Masana ilimi kamar Dr Aliyu Tilde masanin tsarin ilimi kuma tsohon kwamishinan ilimi a jihar Bauchi ya ce daga shekara biyar ya kamata a ce yaro ya soma karatun boko na firamare.
A cewar masanin, galibi ƙasar na bin tsari matakan ilimi ne da ake kira 6-3-3-4 – wato shekara shida a matakin firamare, sai uku a shekarun farko na sakandare da shekaru uku na karshe a matakin sakandare.
Galibi kuma za a yi shekara huɗu a matakin Jami’a.
Dr Tilde ya ce idan yaro ya fara karatun boko yana shekara biyar, zai kasance ya kammala yana da shekara 11. Idan aka ƙara da shekaru shida da ya kamata ya yi a sakandare, zai kasance ya kammala yana da shekara 17.
Ya ce bisa bin tsarin 6-3-3-4 – yana da wahala yaro a ce ya kammala sakandare shekarunsa ba su kai shiga jami’a ba.
Jami’a ta bambanta da sakandare
Karatun Jami'a shi ne mataki na ƙarshe a tsarin karatun Boko da yaro zai yi.
“Kuma ana son ya fara a lokacin da ya kai shekarun balaga wato lokacin da ake ganin ya mallaki hankalinsa.”
“Balaga na da muhimmanci idan yaro zai soma karatun Jami'a saboda akasari zai shiga wani mataki ne da zai yi rayuwa da manyan mutane cikinsu akwai masu aure har da tsofaffi maza da mata.”
“Kuma zai kasance cikin yara balagaggu a aji da ɗaki guda - kuma darasin da zai samu a jami'a na bukatar hankali da bunƙasar kwakwalwarsa da sanin ciwon kai domin Jami’a ta bambanta da firamare da sakandare,” in ji Dr Tilde.
Don haka kiyaye tsarin matakai na karatu a Najeriya zai tabbatar da cewa aƙalla yaro zai shiga Jami'a bai gaza shekara 16 ba.
Ina matsalar take?
Ana zargin iyaye da gaggawar saka yara makaranta tun kafin shekarunsu ba su kai ba, musamman makarantun masu zman kansu wadanda ba na gwamnati ba.
Masana sun ce shekaru na da matuƙar muhimmanci ga karatun yaro, domin ƙwaƙwalwarsa tana da nata tsari na ɗaukar karatu.
A baya, sai yaro ya kai shekara bakwai yake soma karatun boko na firamare. Wannan wata dama ce ga iyaye su fara ba yaransu tarbiya tun daga gida kafin soma karatu.
Amma a wannan zamanin, yara tun suna ƙanana ake fara saka su makaranta musamman idan iyayen dukkaninsu ma’aikata ne.
“Kwanya tana buƙatar ta kai lokacin bunƙasa kuma a hankali take bunƙasa daidai da shekaru kuma an tsara karatun ne daidai da shekarun yaro,” a cewar Dr Tilde.
Duk da cewa ana son yaro ya soma firamare daga shekara biyar, amma wasu yaran kan fara karatun ne a Najeriya tun kafin shekara biyar.
Wannan na faruwa ne saboda tabarbarewar tsari da kuma wanzuwar makarantu masu zaman kansu.
Irin makarantu masu zaman kansu, gwamnati ba ta damu da shata masu iyaka ba ko kuma wani shamaki – kuma akwai wasu na gwamnati da ke kara-zube,” in ji Dr Tilde.
Masanin ya ce wata matsalar ita ce yadda yara ke tsallaken ajujuwa tun daga matakin firamare - inda wasu kan yi shekara hudu maimakon shekara shida a firamare.
“A Sakadare ma wasu kan yi shekara hudu kawai maimakon shekara shida.”
“Wasu tun suna shekara hudu za a fara cewa su yi jarabawar kammala sakandare - daga ƙarshe sai ka ga yara ne ƴan kasa da shekara 15 ke ƙoƙarin shiga jami'a,” in ji masanin.
Ya ƙara da cea irin wannan yana cutar da ɗalibai wanda dole hukumomi su ɗauki mataki.
Me ya kamata a yi?
Kamar yadda ake da tsari na matakan karatu, masana na ganin ya kamata a ƙarfafa su tare da tabbatar da cewa an yi aiki da tsarin.
Ana kuma iya fito da wasu dubaru da za su taimaka wajen magance matsalolin inda Dr Tilde ya ce lokacin da yana kwamishinan ilimi a Bauchi ya yi ƙoƙarin fito da wata hanya ta yadda za a daƙile tsallaken karatun yara.
“Mun yi ƙoƙarin fito da tsarin bayar da lamba ga kowane ɗalibi tun daga matakin firamare - kamar yadda ake ba ma’aikatan jinya lamba,” in ji shi.
Ya ce idan aka ba yaro lamba tun lokacin da ya soma karatun firamare zai ci gaba da amfani da lambar har ya kammala.
“Lambar za ta tabbatar da shekarun da ya fara karatun boko kuma za ta hana shi yin tsallake domin ko ya yi za a gane cewa shekarunsa ba su kai ba.
Masanin ya ce a iya yin wannan tsarin a dukkanin makarantu a matakin jiha da tarayya – “hakan zai taimaka wa gwamnati tattara bayanai tare da samar da kundi kan bayanan daliban da ke karatu da kuma matakin da suke.”
Wasu kuma na ganin sai an soma ƙayyade shekarun soma karatun boko tun daga firamare domin hakan ne zai kasance tsanin ƙayyade shekarun yaro na shiga Jami’a.