Saudiyya ta naɗa Yaya Toure mataimakin kocinta

An wallafa

An naɗa tsohon ɗan wasan tsakiyar Ivory Coast Yaya Toure mataimakin kocin tawagar ƙasar Saudiyya.

Ɗan wasan mai shekaru 40, zai yi aiki tare da Roberto Mancini, wanda ya horar da shi a Manchester City.

A watan Agusta ne aka naɗa Mancini a matsayin kocin Saudiyya kuma ya jagoranci wasanni huɗu tun lokacin.

Toure, wanda ya buga wa City wasa na tsawon shekaru takwas bayan ya sanya hannu a 2010, ya fara horar da ‘yan wasa a shekarar 2019 kuma ya bar aikinsa a kulob ɗin Standard Liege na Belgium.

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Barcelona ya kuma shafe lokaci yana aiki tare da ƙungiyar Donetsk Olympic ta Ukraine, da Grozny ta Rasha, da kuma yin kocin matasa a Tottenham Hotspur.

A lokacin wasansa, Toure ya buga wa Ivory Coast wasanni 101, inda ya lashe gasar cin kofin Afrika a shekarar 2015, da kuma kofuna 18 a wasan ƙwallon ƙafa na ƙungiyoyi a ƙasashen Girka da Sifaniya da Ingila da kuma China.