Real Madrid ta koma ta daya a teburin La Liga bayan cin Cadiz

Jude Bellingham

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Kungiyar Cadiz ta yi rashin nasara a gida a hannun Real Madrid da ci 3-0 a wasan mako na 14 a La Liga da suka fafata ranar Lahadi.

Minti 14 da fara wasan Real ta fara cin kwallo ta hannun Rodrygo, haka suka je hutu kungiyar Santiago Bernabeu ba ta kara ba.

Da suka koma zagaye na biyu ne bayan hutu Rodrygo ya kara kwallo, kuma na biyu da ya zura a raga a fafatawar.

Daga baya ne Jude Bellingham ya ci wa Real na uku na 11 da ya zura a raga jimilla a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Da wannan sakamakon Real ta dare kan teburi da maki 35, bayan wasa 14 a La Liga.

Sai a ranar Litinin Girona za ta karbi bakuncin Athletic Bilbao a karashen wasan mako na 14 a La Liga.

Girona mai maki 34 za ta iya komawa matakinta na farko da zarar ta yi nasara a kan Bilbao ranar Litinin.

Ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, Real za ta karbi bakuncin Napoli a wasan cikin rukuni a Champions League

Daga nan Real za ta yiwa Granada masauki a karawar mako na 15 a gasar ta La Liga.

Atletico Madrid ce ta ukun teburin kakar bana da maki 31, iri daya da na Barcelona ta hudu.