Gundogan zai tafi Bercelona a ƙarshen wata

An wallafa

Kaftin ɗin Manchester City Ilkay Gundogan zai koma ƙungiyar Barcelona, kuma shi ne zai daidaita da sabon kulob ɗin nasa, bayan ƙarewar kwanturaginsa a ƙarshen wannan wata.

Man City ta gabatar wa Gundogan mai shekara 32, sabon kwanturagi amma ana jin cewa ya daidaita a kan wata yarjejeniya da ta fi tsoka ta tsawon shekara uku da zakarun na ƙasar Sifaniya.

Kocin Manchester City Pep Guardiola yana alla-alla ya ci gaba da aiki tare da Gundogan, wanda jigo ne a nasarar kulob ɗin wajen ɗaukan kofi uku a wannan kaka.

Bajamushen ɗan wasan tsakiyar ya buga wasa 51 a kakar wasanni ta 2022 - 23, inda ya ci ƙwallo 11.

Biyu daga ciki su ne ƙwallayen da ya ci a wasan ƙarshe na Gasar FA, inda City ta doke Manchester United, a ciki har da ƙwallon da aka ci mafi sauri a tarihin Kofin FA bayan daƙiƙa 13 kacal.

Ya buga wasa tsawon minti 90 a karawar ƙarshe ta Gasar cin Kofin Zakarun Turai, inda Man City ta ci Inter Milan 1-0, abin da ya sa ta ɗora a kan nasarorinta na gasar Firimiya da Kofin FA a kakar bana.

Gundogan ya shiga ƙungiyar Man City daga Borussia Dortmund a kan kuɗin da aka ba da rahoto sun kai fam miliyan 20 a shekara ta 2016, kuma ya buga wa kulob ɗin wasa 304, ya ci ƙwallo 60.

A tsawon shekara bakwai da ya kwashe a Filin Ƙwallo na Etihad, ya ci kofi 14 - Gasar Firimiya biyar da Gasar Zakarun Turai ɗaya da Kofin FA biyu sai Kofin EFL guda huɗu da kuma Community Shields biyu.

A farkon kakar 2022-23 ne Man City ta naɗa shi matsayin kyaftin bayan ɗan wasan tsakiyar Brazil Fernandinho ya bar kulob ɗin.

'Za a riƙa tunawa Gundogan kamar Silva da Kompany da kuma Toure a Man City'

Sharhi daga Simon Stone, Sashen Wasanni na BBC

A ƙarshe dai, lamarin ya ƙare cikin wani sassauƙan lissafi daga yadda Man City ke kallon lamarin.

E, suna son Gundogan ya ci gaba da zama.

E, Guardiola ya yi ta zazzaga wa Bajamushen kalmomin yabo musamman a makonnin ƙarshe na kakar wasannin mai cike tarihi.

Sai dai City ba za ta iya kashe ko nawa ba ne, don kawai tana so ta ci gaba da zama Gundogan.

Sun yi masa tayin kwanturagin shekara ɗaya da yiwuwar ƙarin kakar wasanni.

Sai dai Barcelona ta yi masa tayin da ya ƙunshi ƙarin shekara ɗaya a kan na Man City.

Gundogan yana da shekara 32, kuma zaƙaƙurin ɗan wasa a City, yana sane da cewa 'yan ƙwallo kaɗan ne za su iya gasa da shi.

Man City, a matsayin ƙungiyar da ta yi nasarar cin kofi uku, suna kan sharafinsu. 'Yan wasa a yanzu na son zuwa su buga ƙwallo da Guardiola.

Ƙungiyar za ta iya samun zaratan 'yan baiwa, kuma ko Kovacic, yana daf da yin haka.

Ƙungiyar Man City cikin bege za ta riƙa tunawa da Gundugan tamkar dai David Silva da Yaya Toure da kuma Vincent Kompany.