Bayern ta yi wa PSG gida da waje a Champions League a bana

Bayern Munich

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Bayern Munich ta doke Paris Germain da cin 2-0 gida da waje a Champions League wasa na biyu zangon 'yan 16 da suka fafata ranar Laraba.

Bayern ta fara cin kwallo ta hannun Eric Maxim Choupo-Moting, bayan da aka koma zagaye na biyu, sannan Serge Gnabry ya kara na biyu daf da za tashi wasan.

Da wannan sakamakon Bayern ta yi nasara a kan PSG sau bakwai a wasa 13 da suka kara tsakaninsu, PSG ta yi nasara a karo shida.

Kungiyar Jamus ta doke ta Faransa da ci 1-0 a wasan farko a bana a gidan PSG.

Kenan Bayern ta kai zagaye daf da na kusa da na karshe a Champions League.

Za a raba jadawalin 'yan kwata fainal ranar 17 ga watan Maris a Nyon, Switzerland.