Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Guimaraes ya tsawaita kwantiraginsa a Newcastle United
Ɗan wasan Newcastle United, Bruno Guimaraes ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar, domin ya ci gaba da taka leda a St James' Park.
Guimaraes, mai shekara 25, ya koma Newcastle daga Lyon a Janairun 2022, wanda kawo yanzu ya buga wasa 67 da cin kwallo 11.
Ɗan kwallon tawagar Brazil , ya bayar da gudunmawar da Newcastle ta samu gurbin shiga gasar Champions League a karon farko bayan shekara 20.
Tun farko kwantiraginsa zai kare a 2028 - kenan ƙarin kaka biyu a kan wadda yake da ita tun farko.
Eddie Howe ya ce tun bayan da Guimaraes ya koma Newcastle United, kungiyar sai samun ci gaba take yi.
Newcastle United za ta buga wasan Premier League a gidan West Ham ranar Lahadi a wasan mako na takwas.