Sau biyu ana yi wa Casemiro jan kati a Premier League

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Southampton sun tashi 0-0 a gasar Premier League ranar Lahadi a Old Trafford.
United ta karasa wasan da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Casemiro jan kati a minti na 34.
Karo na biyu kenan da dan wasan Brazil ya karbi jan kati a Premier League, bayan wanda aka yi masa a karawa da Crystal Palace ranar 4 ga watan Fabariru.
United ce ta yi nasara da cin 2-1 a wasan, inda Bruno Fernandes da Marcus Rashford suka ci mata kwallo, Palace ta zare daya ta hannun Jeffrey Schlupp .
Casemiro, wanda ya koma United daga Real Madrid kafin fara kakar bana, ya fara buga Premier ranar 27 ga watan Agustan 2022 a wasan da United ta ci Southampton 2-1 a St Mary.
Ya fara karbar katin gargadi a Premier League a bana a wasan da United ta tashi 0-0 da Newcastle United ranar 16 ga watan Oktoba a Old Trafford.
Kawo yanzu ya karbi kati mai ruwan dorawa karo biyar a Premier da daya a FA Cup da biyu a Europa League da daya a League Cup tun da ya fara yi wa United tamaula.
Casemiro ya fara ci wa United kwallo a wasan Premier da United ta tashi 1-1 a gidan Chelsea ranar 22 ga watan Oktoban 2022.
Ya kuma ci Bournemouth a karawar da United ta yi nasara da cin 3-0 a Old Trafford ranar 3 ga watan Janairun 2023 a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Casemiro ya zura kwallo biyu a raga a FA Cup a karawar da United ta doke Reading 3-1 ranar 28 ga watan Janairu.
Haka kuma ya ci kwallo a wasan da United ta doke Newcastle United 2-0 ta dauki Carabao Cup a kakar nan.











