Nasarar Super Eagles da Ƙaddamar da sabbin jiregen yaƙi da wa'adin ƙungiyar kwadago

An wallafa

Najeriya ta kai wasan ƙarshe a Afcon bayan doke Afirka ta Kudu

Najeriya ta samu nasarar zuwa wasan ƙarshe a gasar cin koin ƙwallon ƙafa na nahiyar Afirka, 2023 da ke gudana a Ivory Coast.

Najeriyar ta kai wasan na ƙarshe ne bayan ta doke Afirka ta Kudu a bugun fanareti da ci 4-2.

Hakan na nufin Najeriya za ta kara ne da mai masaukin baƙi Ivory Coast wadda ita kuma ta doke Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo a tasu karawar ta gaf da ƙarshe da ci 1-0.

An je bugun fanareti ne a wasan Najeriya da Afirka ta Kudu ne bayan kwashe minti 120 ana fafata wasa ba tare da an samu ƙasar da ta zura ƙwallaye mafi yawa ba.

Gwamnatin Abuja ta bai wa masu zama ƙasan gada wa'adin su tashi

Hukumar kula da birnin Abuja ta bai wa ɗaruruwan mutane da ke zama a ƙarƙashin gadojin da ke birnin mako guda su tashi ko kuma su fuskanci fushin hukumar.

Mai taimaka wa ministan birnin na Abuja kan muhalli da kawar da shara, Fred Kpakol ya ce sun ɗauki matakin ne sakamakon koken da mazauna birnin ke yi kan ƙwace da fashi da ake yi wa al'umma.

Fred Kpakol ya ce gadojin da ake fuskantar wannan mastaala da aka umarci waɗanda ke zaune a kasansu sun haɗa da gadojin unguwannin Garki, Wuse II, Maitama, da Wuse.

Tinubu ya ƙaddamar da sabbin jiregen yaƙi don magance matsalar tsaro

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen mastalar tsaro a ƙasar ta hanyar ƙaddamar da wasu sabbin jirage masu saukar ungulu kirar T-129 ATAK guda biyu da kirar King Air 360ER Beechcraft a barikin sojin saman Najeriya da ke birnin Makurdi a jihar Benue..

Da yake magana ta bakin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar sayen waɗannan sabbin jiragen masu saukar ungulu domin inganta yaƙin da rundunar sojojin saman Najeriya ke yi a ƙasar da yankin yammacin Afirka.

Badaru Abubakar, ministan tsaro ya yaba wa ƙoƙarin shugaba Tinubu na mayar da zaman lafiya a fadin ƙasar, ya kuma gode masa bisa jajircewarsa da goyon bayan da yake bai wa rundunar sojin ƙasar duk da kalubalen da take fuskanta.

An gano inda ake sayar da jarirai a Anambra

Gwamnatin jihar Anambra da ke kudancin Najeriya ta ce ta gano wani gidan sayar da jarirai tare da ceto wasu mata masu ciki biyar a garin Umunya da ke yankin karmar hukumar Oyi.

An gano gidan ne a wani sumamen hadin guiwa tsakanin ma'aikatar lafiya da hukumoin tsaron jihar.

Da ya ke bayani ga manema labarai, kwamishinan lafiya a jihar Dr. Afam Obidike ya ce sun gano cewar gidan sayar da yaran na gudanar da harkokinsa ta hanyar basaja a masatyin asibiti, nan kuwa cibiyar safarar jarirai ce.

Ya bayyana sunan gida da "Asibitin Mother Child and Maternity" da ke kan titin jami'ar Tansian, da a Umunya.

Kungiyar kwadago ta yi watsi da karin 10,000 da gwamnan Jigawa ya yi wa ma'aikata

Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa reshen jihar Jigawa ta yi watsi da tukwicin 10,000 da gwamnatin jihar za ta bai wa ma'aikatanta a matsayin kuɗin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Wannan yana kunshe a cikin wata sanarwar da aka saki bayan kammala taron kungiyar da aka yi ranar Talata a Dutse.

Sanarwar wadda shugabannin kananan hukumomi da kuma sakatarorin ƙungiyar ƴan kwadago ta NLC da TUC reshen jihar suka saka hannu ta fasalta yadda gwamnatin ta yi azarɓaɓin yanke hukunci kan bada tukwicin tun da ba su cimma yarjejeniya ba.

An ceto mutum 20 daga hannun masu garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta ce dakarunta sun ceto wasu mata kusan 20 daga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina tare da mika su hannun hukumomin jihar.

Sojojin sun ce sun samu nasarar kubutar da mutanen ne yayin wasu hare-haren da suka kai kan maboyar ‘yan bindigar a dazukan ‘yan-tumaki da Dan-Ali.

Hakan dai na zuwa ne bayan sace wasu mata 53 da ke kan hanyarsu ta zuwa kai amarya a yankin karamar hukumar Sabuwa.

A lokacin da ya yi wa BBC ƙarin bayani, kwamishinan harkokin tsaro na jihar Katsina, Nasir Mu'azu ya ce babu tabbas kan lokacin da aka sace mutanen da aka ceton.

Sai dai ya bayyana cewa mutanen da aka ceton ƴan asalin ƙaramar hukumar Musawa ne da ke jihar.

NNPCL ya musanta shirin ƙara kuɗin man fetur

Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya musanta duk wani yunƙuri na ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar.

A baya-bayan nan masu ababen hawa na fuskantar dogayen layuka a wasu gidajen mai a wasu yankunan ƙasar, musamman a kudancin ƙasar, sakamakon fargabar da ake yi cewa hukumomi za su ƙara farashin man.

To sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya fitar mai ɗauke da sa hanun jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar, ya buƙaci 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu.

''Ba za a ƙara kuɗin man fetur ba'', kamar yadda sanarwar kamfanin ta tabbatar.

Gargaɗin boye abinci da Gwamnati ta yi

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi 'yan kasuwar da ke da ɗabi'ar ɓoye kayan abinci a daidai lokacin da talakawan ƙasar ke cikin matsin rayuwa.

Ministan yaɗa labaran ƙasar Muhammad Idris ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan taron gaggawa kan halin matsin rayuwa da tsadar abinci da 'yan ƙasar ke ciki.

Ministan ya ce gwamnati a nata ɓangare za ta fito da metri ton 42,000 na abinci daga rumbunan ma'aikatar harkokin noma.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke cikin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fuskanta a cikin makonnin baya-bayan nan.

''Ma'aikatar harkokin noma na da masara da gero da nau'in gari a rumbunan ajiyarta da ke sassan ƙasar daban-daban domin raba wa 'yan ƙasar nan ba da jimawa ba'', in ji ministan.

'Nan ba da jimawa ba farashin kayan abinci zai sauka'

Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ya ce majalisar na sane da halin matsalar tsaro da tsadar rayuwa da 'yan ƙasar ke fuskanta.

Honarabul Tajudeen Abbas ya ce a ɓangarensu na majalisa ba za su zuba wa ɓangaren zartaswa ido ba har sai an samu mafita.

Kakakin majalisar ya tabbatar wa da BBC cewa za a shawo kan ƙalubalen da ake fuskanta nan ba daɗewa ba.

''Majalisa za ta yi duk abin da ya kamata domin ganin an samu sauƙi a matsalar tsaro da tsadar rayuwa da ke fuskanta a ƙasar nan''.

Kakakin majalisar ya ce majalisa ta za kirawo duka masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin magance matsalar tsaron da ake ciki.

Honarabul Tajedeen Abbas ya ce 'yan majalisar na sane da irin halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke ciki, kuma suna duk mai yiwuwa domin magance matsalar.

Ziyarar Dangote a Kano

Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya alƙawarta tallafa wa tsare-tsaren manunfofin taimaka wa al'umma da ci gabansu, don magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.

Dangote ya yi wanna alƙawarin ne a lokacin da ziyarci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf a gidan gwamnatin jihar ranar Juma'a.

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce Dangote ya ce yana sane da halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke fuskanta.

Dangote ya alƙwarta bayar da tallafi don inganta fannonin lafiya da ilimi da hanyoyin yaƙi da talauci ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.

Attajirin ɗan kasuwar ya alƙawarta yin aiki kafaɗa dakafaɗa da gwamnatin jihar don bunƙasa ci gaban al'ummar jihar.