Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
DSS ta ce masu shirin kafa gwamnatin riƙo a Najeriya su janye makircinsu
Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya ta ce ta shaida wasu jiga-jigai da ke kitsa wata maƙarƙashiya don kafa gwamnatin riƙon ƙwarya a ƙasar.
Hukumar ta ce maƙarƙashiyar, wadda wasu ke izawa ba kawai aba ce da ta saɓa wa doka ba, wani ƙoƙarin masu jamhuru ne na kifar da tsarin mulkin Najeriya da kuma jefa ƙasar cikin wani rikici da za a iya kauce masa.
Ta ce tunanin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya, abu ne da ba za a amince da shi ba, a tsarin dimokraɗiyya da kuma muradin zaman lafiyar al'ummar ƙasar.
A saƙon da ta wallafa a shafinta na Tuwita ɗauke da sa hannun jami'in yaɗa labaran hukumar, Peter Afunanya, DSS ta ce tun bayan zaɓukan ƙasar da aka kammala cikin kwanciyar hankali, ake ta raɗe-raɗin kafa gwamnatin riƙo.
Sai dai DSS ba ta fito kai tsaye ta ce ga 'yan siyasar da take zargi da shirya wannan maƙarƙashiya ba.
Ta dai ce masu kitsa makircin, a jerin tarukan da suke yi, suna auna batutuwa da dama ciki har da yadda za su ɗauki nauyin zanga-zanga maras iyaka a manyan birane ta yadda daga bisani za a ayyana dokar ta-ɓaci.
Wani abin kuma shi ne, su samu umarnin kotu don hana rantsar da sabbin shugabannin da aka zaɓa da ƴan majalisa a matakin tarayya da jihohi.
'Yan adawa a Najeriya sun soki lamirin sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara a watan Fabrairun 2023. Sun yi zargin cewa zaɓen yana cike da kura-kurai, kuma an tafka maguɗi, baya ga amfani da tashe-tashen hankula don yin tarnaƙi ga masu zaɓe.
Haka zalika, manyan 'yan adawan da suka yi takara da Bola Tinubu kamar Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP da Peter Obi na Labour Party duk sun shigar da ƙara a gaban kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓe suna ƙalubalantar nasarar Tinubu.
Ita dai Hukumar DSS ta bayyana goyon baya ga ƙudurin Shugaba Buhari mai barin gado wajen tabbatar da ganin an miƙa mulki ba tare da wani tashin hankali ba, kuma ta ce za ta yi aiki tuƙuru don ganin tabbatar hakan.
Ta kuma ce tana goyon bayan kwamitocin miƙa mulki da shugaban ƙasar ya kafa da kuma waɗanda aka kafa a jihohi.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta yi aiki da sauran hukumomin tsaro don ganin an yi bikin miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
DSS ta kuma gargaɗi waɗanda ta kira masu shirin daƙile dimokraɗiyyar Najeriya, su janye ƙudurinsu.
Sannan ta buƙaci hukumomi a ɓangaren shari'a da kafofin labarai da kuma ƙungiyoyin fararen hula su yi taka tsantsan don kada a yi amfani da su wajen tayar da fitina da ruguza zaman lafiyar ƙasar.
A ranar Talata ma, sai da gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa ƴan ƙasar cewa duk da ƙalubalantar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da wasu jam'iyyun adawa ke yi a kotu, ba za a fasa miƙa mulki hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ba.
Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Gida Mustapha, ya ce sun shirya tsaf don miƙa mulki a ranar 29 ga watan Mayu cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba.