Real Madrid na shirye-shiryen zuwa gidan Celta Vigo

Asalin hoton, Real Madrid
Real Madrid za ta ziyarci Celta Vigo, domin buga wasan mako na uku a gasar La Liga ranar Juma'a 25 ga watan Agusta.
A cikin makon nan Real ta yi atisaye uku, domin ganin ta taka rawar gani a gidan Celta at Balaídos.
'Yan wasa sun motsa jiki, an kuma raba kwallo, sannan suka yi tabe-tabe a gefen fili, an kuma yi atisaye tare da Ceballos da Mendy.
Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki shida, bayan da ta je ta doke Athletic Bilbao 2-0 da kuma cin UD Almeria 3-1.
Real Madrid ta doke Celta Vigo gida da waje a kakar da ta wuce, wadda ta ci Celta 2-0 a gida, sannan Real ta yi nasarar cin 4-1 a gidan Celta.
Karawar da kungiyoyin suka yi a 2022/2023
Gasar La Liga Asabar 22 ga watan Afirilun 2023
- Real Madrid 2 - 0 Celta Vigo
Gasar La Liga Asabar 20 ga watan Agustan 2022
- Celta Vigo 1 - 4 Real Madrid
Wasannin mako na uku da za a buga
- Las Palmas da Real Sociedad
- Celta Vigo da Real Madrid
Ranar Asabar 26 ga watan Agusta
- Cadiz da Almeria
- Granada da Real Mallorca
- Sevilla da Girona
Ranar Lahadi 27 ga watan Agusta
- Villarreal da Barcelona
- Valencia da Osasuna
- Athletic Bilbao da Real Betis
Ranar Litinin 28 ga Agusta
- Getafe Deportivo Alaves
- Rayo Vallecano da Atletico de Madrid









