Rubiales ya ƙi ajiye aikinsa kan sumbatar 'yar wasa

An wallafa

Luis Rubiales ya ƙi sauka daga mukaminsa na shugaban hukumar kwallon kafa ta Spaniya, sakamakon ce-ce-ku-ce kan halayyar da ya nuna a wasan ƙarshe na cin Kofin Duniya ta Mata a ranar Lahadi.

Rubiales, mai shekara 46, ya sumbaci 'yar wasan gaba Jenni Hermoso a lebe bayan da Spain ta doke Ingila da ci 1-0.

Tun da farko dai ya damƙe gabansa a lokacin da yake murnar kammala wasan.

Rubiales ya nemi gafara ranar Litinin kan sumbatar 'yar wasan da ya yi a kafin hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta bude bincike a kansa ranar Alhamis.

A ranar Juma'a ya nemi afuwa kan cewa ya kama gabansa a lokacin da yake murna a bangaren VIP na filin wasan Stadium Australia, yayinda Sarauniya Letizia ta Sifaniya da 'yarta mai shekaru 16 ke tsaye kusa da shi.

Daga farko dai ya nemi kare kansa daga abin da ya aikata, yana mai cewa ya yi ƙoƙarin jajanta wa Hermoso ne bayan golan Ingila Mary Earps ta kama fanaretin da ta buga.