Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An ƙara dakatar da Van Dijk wasa ɗaya da tarar fam 100,000
An ƙara dakatar da kyaftin ɗin Liverpool, Virgil van Dijk wasa ɗaya da cin tarar fam 100,000, sakamakon halin rashin ɗa'a, bayan ba shi jan kati.
An kori dan kwallon tawagar Netherlands a minti na 28, bayan da ya yi wa Alexander Isak ƙeta a gasar Premier League da Newcastle United.
Tun farko an dakatar da Van Dijk wasan da Liverpool za ta kara da Aston Villa ranar 3 ga watan Satumba, yanzu kuma ba zai yi wasan da za ta yi da Wolverhampton ba ranar 16 ga watan Satumba.
Mai tsaron bayan ya faɗa wa alkalin wasa John Brooks kalamai lokacin da zai bar fili a St James Park.
Haka kuma Van Dijk, mai shekara 32 ya yi cacar baki da alkalin wasa mai jiran ko-ta-kwana a lokacin da zai bar filin.
''Jan katin farko da na karɓa a Liverpool kenan, abin ya ba ta min rai a lokacin da ta kai na yi abubuwan da ba su kamata ba.
''Na nemi afuwa a wajen alkalan wasan nan take bayan tashi daga fafatawar na kuma ɗauki alhakin laifin dukkan abin da aka tuhemi.'' in ji Van Dijk.
Liverpool ce ta doke Newcastle United da ci 2-1 a wasan mako na huɗu a babbar gasar tamaula ta Ingila.