Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PSG na son Silva, Arsenal na lallaɓar West Ham a kan Rice
Dan wasan Manchester City, Bernardo Silva shi ne na daya a cikin wadanda Paris St-Germain ke son saye a yanzu a kokarin da kungiyar ta Faransa ke yi na maye gurbin Lionel Messi. (Le Parisien)
A shirye Arsenal take ta bai wa West Ham kudin da kungiyar ba ta taba samu a sayar da dan wasa ba, fam miliyan 90 domin sayar mata da Declan Rice, sannan kuma watakila Granit Xhaka, ya kasance daya daga cikin wadanda Gunners din za su sayar. (Mail)
Dan wasan tsakiya na Argentina Alexis Mac Allister, wanda ake danganta shi da Liverpool da Manchester United, yana son tafiya kungiyar da za ta buga gasar Zakarun Turai idan har zai bar Brighton a bazarar nan. (Athletic)
Mauricio Pochettino da ake sa ran ya kammala zama sabon kociyan Chelsea zai tattauna da Mason Mount domin ya shawo kan dan wasan na Ingila ya tsawaita zamansa a kungiyar kasancewar yarjejeniyarsa ta yanzu za ta kare ne a bazarar 2024. (Football Insider)
Ana ganin Barcelona na son dan wasan tsakiya na Wolves Ruben Neves kuma idan har za ta sayar da shi a bazara mai zuwa to kungiyar za ta karbi kudin da bai gaza fam miliyan 45 ba. (Telegraph)
Newcastle United ta kara nuna sha'awarta a kan matashin dan wasan tsakiya na Hungary Dominik Szoboszlai, wanda kwantiraginsa da RB Leipzig ya tanadi sayar da shi ga duk kungiyar da take so a kan yuro miliyan 70, to amma kuma kungiyoyin biyu har yanzu ba su yi wata magana ba a kai. (Sky Sports)
Haka kuma Newcastle din na son matashin dan wasan tsakiya na Chelsea Conor Gallagher, sannan kuma ana ganin Magpies din za ta fuskanci gogayya da Tottenham a kan wani dan wasan na Ingila shi ma kuma tauraron Leicester City James Maddison. (Mail)
Bayern Munich da Borussia Dortmund na son dan wasan tsakiya na Mexico Edson Alvarez, wanda kila Ajax ta sayar da shi a kan fam miliyan 30. (SPORT1)
Ana sa ran Manchester United ta rabu da 'yan bayanta biyu 'yan Ingila Phil Jones da Axel Tuanzebe, a bazaran nan. (Manchester Evening News)
Sannan kuma Manchester United din na tunanin sayen mai tsaron ragar Borussia Dortmund Gregor Kobel, amma kuma ana ganin kungiyar ta Jamus za ta gabatar wa da golan na Switzerland sabon kwantiragi. (Independent)
West Ham na son nada darektan wasanni domin rage wa Mark Noble yawan aikin da ke gabansa tare kuma da rage tasirin kociyan kungiyar David Moyes a kan harkar cinikin 'yan wasa idan har Moyes din ya tsaya. (Guardian)
Sannan Hammers din na sanya ido a kan dan wasan tsakiya na Amurka Yunus Musah, wanda ke kokarin taimaka wa Valencia kauce wa faduwa daga gasar La Liga. (Mail)
Mai tsaron ragar Brentford da Sifaniya David Raya, mai shekara 27, kusan shi ne na daya a wadanda Tottenham ke sa ran saye, kasancewar ana ganin golan Faransa Hugo Lloris, mai shekara 36, zai bar kungiyar a bazaran nan. (Telegraph)
Watakila Brentford ta sayi mai tsaron ragar Netherlands Mark Flekken, wanda kwantiraginsa da Freiburg ta Jamus ya tanadi sayar da shi a kan fam miliyan 11.3 (Sport1)