Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Barcelona da Bilbao za su buga Copa del Rey ranar Laraba
Athletic Bilbao da Barcelona za su fafata a wasan quarter finals a Copa del Rey ranar Laraba.
Barcelona ta kawo wannan matakin bayan da ta doke Unionistas Salamanca 3-1 ranar Alhamis.
Ita kuwa Athletic Bilbao ta yi nasarar fitar da Deportivo Alaves da cin 2-0 ranar Talata a karawar zagayen ƴan 16.
Barcelona da Athletic Bilbao sun fafata a bana a gasar La Liga ranar 22 ga watan Oktoban 2023, inda kungiyar Camp Nou ta ci 1-0.
Saura minti 10 su tashi daga karawar Barcelona ta ci kwallon ta hannun Marc Guiu.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey a tarihi mai 31 jimilla, Athletic Bilbao ce ta biyu mai 23.
Real Madrid ce ta uku mai 20 da kuma Atletico Madrid ta hudu a yawan daukar Copa del Rey mai 10.
Girona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 52, sai Real Madrid mai maki 51 da kuma Barcelona ta uku mai maki 44.
Athletic Madrid ce ta hudu da maki 41, iri daya da na Bilbao, wadda take ta biyar a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Wasannin quarter finals da za a buga a Copa del Rey
Ranar Talata 23 ga watan Janairun 2024
- Celta de Vigo da Real Sociedad
Ranar Laraba 24 ga watan Janairu 2024
- Real Mallorca da Girona
Athletic Bilbao da Barcelona
Ranar Alhamis 25 ga watan Janairun 2024
- Atletico Madrid da Sevilla