Abin da ya sa masarautar Funakaye ta fita daban a Najeriya
Abin da ya sa masarautar Funakaye ta fita daban a Najeriya
An wallafa
BBC ta ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Funakaye da ke garin Bajoga na jihar Gwambe domin ganin yadda mawaka da mabusan fada ke gudanar da ayyukansu na sarauta.
Makaɗan fada wani nau’i ne na musamman a rukunin makaɗan gargajiya na ƙasar Hausa, waɗanda ba kowa suke yi wa waka ba, sai sarakuna da sauran waɗanda suka shafi sarauta.
Waɗannan makaɗa dai sukan yi amfani da kayan kiɗa ne irin su ganga da algaita da kakaki da dai sauransu.



