'Halin da muka shiga daga Sudan zuwa Najeriya'
'Halin da muka shiga daga Sudan zuwa Najeriya'
An wallafa
A yayin da Najeriya ta kammala ƙwasar ɗalibanta da ke Turkiyya, wasu ɗaliban da suka koma ƙasar sun bayyana irin halin da suka shiga a lokacin da suke Sudan.
Muhammad Kabiru ɗaya ne daga cikin ɗaliban Najeriya da suka koma ƙasar daga Sudan, ya kuma ce sun ga abubuwa daban-daban a kan hanyarsu ta barin Sudan.
Ya ce a farkon yaƙin sun zauna a gida saboda ba a fita waje, saboda a cewarsa baya ga yaƙin akwai kuma ɓata-gari waɗanda za su far wa mutum idan sun gan shi a waje.
Ya ce a Port Sudan sun riƙa kwana a masallaci kafin a kwashe su zuwa Najeriya.
Dalibin ya ce sun kwashe mako guda a Port Sudan kafin su samu damar a kwashe su zuwa Najeriya.




