Man United ta ƙyalla ido kan Lookman, Wolves na son Sancho

Asalin hoton, Getty Images
Wolves ta bayyana a matsayin mai fafutukar sayen ɗanwasan Manchester United Jadon Sancho mai shekara 25 wanda yake zaman aro a Chelsea, a bazara. (Football Transfers)
Ɗanwasan Manchester United da Argentina Alejandro Garnacho, 20, ya bayar da haske kan yunƙurin da yake a bazara ta hanyar sanya katafaren gidansa na fam miliyan 3.85 a kasuwa shekara ɗaya bayan siyan kadarar. (Sun)
Manchester United na ƙyalla ido kan ɗanwasan Atalanta Ademola Lookman, mai shekara 27, domin bunƙasa tawagarsu a ɓangaren zura ƙwallo. (Caught Offside)
Sporting za ta kasance cikin niyyar rage farashin da ta yi wa ɗanwasan gaba na Sweden Viktor Gyokeres daga fam miliyan 85 zuwa kusan fam miliyan 59 yayin da Arsenal da Manchester United har yanzu suke zawarcinsa. (Athletic - subscription required)
Juventus na ƙara ƙaimi kan sayen ɗanwasan Najeriya Victor Osimhen, 26, a wannan bazarar amma Manchester United a shirye take ta yi gogayya da ƙungiyar wajen ɗauko ɗanwasan Napoli wanda yake zaman aro a Galatasaray. (Teamtalk)
Arsenal ta janye zaƙuwarta kan ɗanwasan Newcastle Alexander Isak mai shekara 25 wanda Magpies ke shirin yi masa tayin sabon kwantiragi. (Chronicle)
Bayer Leverkusen ta sa ƙaimi kan mai tsaron ragar Sifaniya Joan Garcia mai shekara 23 da Arsenal ita ma ke farautarsa. (Bild via Get German Football News)
Inter Milan ba ta da sha'awar sayen ɗanwasan tsakiya na Belgium Kevin de Bruyne mai shekara 33 idan ya bar Manchester City a bazara saboda shekarun ɗanwasan. (Calciomercato - in Italian)
Real Madrid a shirye take ta tsawaita kwantiragin Antonio Rudiger mai shekara 32 har zuwa 2026 duk da zawarcinsa da ƙungiyoyin Saudi Pro League ke yi. (Florian Plettenberg)
Chelsea ba ta da burin cefanar da ɗanwasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez a bazara, inda ɗanwasan mai shekara 24 ya kasance muhimmin ɓangare na shirinsu. (Fabrizio Romano)
Xabi Alonso ya gamsu ya ci gaba da zama a matsayin kocin Bayer Leverkusen inda kocin mai shekara 43 ke farincikin dakon damarsa ta bin sahun Carlo Ancelotti da ke lura da Real Madrid. (Relevo - in Spanish)










