Ta yaya za a ceci yaron da ya ƙware?
Ta yaya za a ceci yaron da ya ƙware?
An wallafa
Ƙwarewa na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke jawo mummunan rauni ko mutuwa a ƙananan yara, musamman waɗanda ba su kai shekara biyar ba.
Ƙwarewa na iya faruwa cikin ƙanƙanin lokaci ko da a lokacin cin abinci, lokacin da yaron yake shan mama, lokacin wasa, ko ma lokacin barci.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, dubban yara a faɗin duniya na rasa rayukansu duk shekara ta dalilin ƙwarewa ko shaƙewa saboda hanyoyin numfashi ne ke toshewa.
Dalilin haka ne BBC ta tuntuɓi Dr. Zulaihat Hassan Nasiha, wata likita a Najeriya, wadda ta bayyana muhimman matakan taimako da kowanne iyaye ko mai kula da yara ya kamata ya sani idan yaro ya shaƙe.



