Najeriya na dab da naɗa sabon kocin Super Eagles

    • Marubuci, Oluwashina Okeleji
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sports writer
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Alamu sun fara nuna cewa an kusa kawo ƙarshen tata-ɓurzar da ake yi kan zaɓen wanda zai cigaba da jan ragamar horar da ƴan wasan Super Eagles na Najeriya, duk da cewa har yanzu akwai tsaikon da ake fuskanta kan cire ɗaya daga cikin mutane biyu da suka rage.

Tawagar Super Eagles ba ta da koci tun bayan da Finidi George ya ajiye aikinsa bayan wasa biyu kacal a cikin kwatiraginsa ta shekara biyu.

Finidi yana cikin ƴan wasan Najeriya da suka lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka (Afcon) ta shekarar 1994, sannan ya taɓa riƙe matsayin na riƙon ƙwarya a wasan sada zumunta a watan Maris.

Wasa ɗaya kawai ya samu nasara a cikin huɗu da ya jagoranci tawagar, sannan Benin ta yi nasara kan Najeriya da ci biyu da ɗaya a wasa na ƙarshe da ya jagoranta, ya sa yanzu Najeriya ce a ƙarshen teburi a rukuninta ne neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Bayan raɗe-raɗin da ake ta yi, da kuma sa hannun Ministan Wasanni na ƙasar, yanzu an ware mutum biyu da za a zaɓa ɗaya a cikinsu: Janne Andersson ɗan Sweden da Herve Renard ɗan Faransa.

Sai dai ko ma wane ne ya zama sabon kocin, ya san da sanin cewa lokaci na ƙoƙarin ƙure wa Najeriya, kasancewar za a fara wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka a ranar 7 ga Satumba.

Andersson na son aikin-amma yana buƙatar lokaci

Andersson zai yi kyau da yanayin tawagar Najeriya saboda da tarihinsa, da rashin tsadarsa.

A bara, kocin mai shekara 61 ya ajiye aikin horar da tawagar ƙasar Sweden, inda ya kai wasan kwata final a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2018, sannan ƙasar ta kai zagaye na biyu a Gasar Nahiyar Turai ta 2020.

Sai dai a ƙarshe-ƙarshen zangonsa, an yi ta samun kwan-gaba-kwan-baya, wanda hakan ya sa ya ajiye aikinsa a Nuwamba bayan ya gaza jagorantar ƙasar zuwa samun gurbin a Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022 da Kofin Nahiyar Turai ta 2024.

Shi kuma Anderson, wanda Sweden kawai ya taɓa horaswa, ya taɓa lashe gasar Sweden da ƙungiyar IFK Norrkoping, sannan an ce yana sha'awar horas da tawaga a Afirka, duk da cewa ana fargabar ba shi da ƙwarewar horaswa a wajen ƙasarsa Sweden.

Wasu kuma cewa suke yi akwai damuwa ganin yadda ya ƙare da tawagar Sweden, amma duk da haka NFF ta amince cewa Anderson yana da ƙwarewar da ake buƙata domin jan ragamar tawagar.

Yadda ya dawo da Zlatan Ibrahimovic buga ƙallo a tawagar Sweden, bayan tsohon ɗan wasan na AC Milan da Barcelona ya fito fili ya soke shi, ya sa ana nuna alamar tambaya a kan ƙarfin gwiwarsa.

Wata matsalar da yake fuskanta ita ce, Anderson ba zai iya fara aiki ba sai a cikin watan Satumba saboda wasu dalilansa.

Zuwa wannan lokacin an riga an buga wasannin neman gurbin shiga Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka ta 2025 tsakanin Najeriya da Benin da Rwanda.

Sai dai za a iya yin tsarin da mataimakinsa, Peter Wettergren zai yi aiki da wani kocin riƙon ƙwarya ɗan Najeriya - wataƙila Augustine Eguavoen- a waɗannan wasannin.

Shin NFF za ta iya biyan Renard?

Renard ya fi shahara a cikin biyun - amma zai fi wahalar ɗauka a matsayin.

Ɗan Faransan ya samu nasarori sosai a ƙwallon Afirka, inda ya zama mutum ɗaya tilo da ya taɓa lashe kofin nahiyar Afirka da ƙasashe biyu daban-daban.

Haka kuma Renard ya jagoranci Maroko da Saudi Arabiya a Gasar Cin Kofin Duniya na 2018 da 2022 bi da bi, inda ya jagoranci Saudi Arabia ta doke Ajantina a wasan rukuni.

Aikinsa na ƙarshe-ƙarshen shi ne jagorantar tawagar matan Faransa, inda suka kai kwata final a Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata a 2023 da kuma gasar Olympics.

Kwanan nan ya nemi gurbin aikin horar da tawagar Amurka, amma bai samu ba, amma kocin mai shekara 55 na samun zawarci daga ƙasashen Turai da Afirka da ƙasashen Asia, duk da cewa ba ya neman aiki ido rufe.

Masar ta shirya biyan shi albashin dala miliyan biyu (£1.5m) a shekara, kuɗin da Najeriya ba za ta iya biya ba.

Kuɗaɗen da yake buƙata sun yi yawa, inda wani babban jami'in NFF ya bayyana da "abu mai kamar wuya".

Duk da matsalar kuɗin, ana cigaba da kallon Renard a matsayin wanda ya fi dacewa da horas da tawagar saboda ƙwarewarsa da kuma yadda ya ke da tarihin lashe kofuna a ƙwallon Afirka.

Shi kan shi zai yi murnar jan ragamar ɗaya daga cikin manyan ƙasashen nahiyar.

Hanya mai cike da tangarɗa

Duk wanda ya samu nasarar zama kocin, lallai akwai jan aiki a gabansa.

Samun gurbin shiga Gasar Kofin Duniya da aka yi zaton zai yi sauƙi, yanzu ya zama wani jan aiki, inda Rwanda ta ke jan ragamar rukunin na C, sannan kuma Zimbabwe ce kawai ake ganin duba da tarihi, take yi wa Najeriya sauƙin dokewa.

Yadda Super Eagles ta kai wasan ƙarshe na Afcon 2023 da rashin nasararta ba a yi tsammani ba, sannan kuma duba da abubuwan da suka biyo baya, za a iya cewa ana samun koma-baya ne.

Wannan ba ya rasa nasaba da rashin kayan aiki na zamani da ɓoye-ɓoyen da ake yi na harkokin kuɗaɗe a wajen gudanar da harkokin ƙwallon ƙafa a Najeriya.

Yanzu haka tawagogin Najeriya na mata da maza ba su da filin wasa na dindindin, inda yawancin wasanninsu na ƙarshe-ƙarshen nan aka buga a Uyo saboda Filin Wasan Goodswill Akpabio ne kaɗai filin wasan da ya cika sharuɗɗan Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka.

Haka kuma akwai batun bin bashin da ƴan wasan suke yi da alawus-alawus.

Waɗannan abubuwan suna cikin abubuwan da suke janyo tsaiko, da za su iya sanyaya gwiwar wanda ya ke da sha'awar zama kocin ƙasar.