Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yajin aikin ASUU ya zame mana masifa'
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC, Abuja
- An wallafa
“Wannan yajin aiki na malaman jami’o’i ya yi matuƙar taɓa mu ɗalibai, don ni har sai da ta kai wani abokina ƙiri-ƙiri ya fara shaye-shaye saboda tsabar shiga damuwa,” in ji Ibrahim Yunusa, ɗalibi a Jami’ar Umaru Musa Ƴar adua a jihar Katsina.
Ibrahim ya ce ya lura abokin nasa, wanda ba zai so bayyana sunansa ba, ya fara tu’ammali da miyagun ƙwayoyi tun wata uku da fara yajin aikin, “wanda a da ba halayyarsa ba ce sam-sam”.
Ɗalibin ya shaida wa BBC Hausa hakan ne a wani shiri da ta nemi jin ra’ayoyin mutane kan muhimman fannoni da suka fi shafar ƴan ƙasar, gabanin zaɓukan 2023.
Matashin mai shekara 25, ya ce a sanin da ya yi wa abokin nasa wanda suke ƙut da ƙut, ko sigari ba ya sha, amma a yanzu abin na neman zarce hankali.
“Da na tuntuɓe shi don yi masa faɗa kan sabon halin da ya fara din, sai ya ce wai na ƙyale shi damuwa ce ta yi masa yawa.
“Ga dukkan alamu wasu sabbin abokai da ya fara bi ne suka ɗora shi a kan wannan hanyar, kuma duk rashin abin yi ne ya jawo hakan” ya ce.
Yawanci matasa kan samu kansu a yanayi na shaye-shayen ƙwayoyi ne sakamakon damuwa da suke samun kansu a ciki, ko rashin abin yi, al’amarin da ya zama ruwan dare a Najeriya.
Tun watan Fabrairun shekarar 2022 ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ta shiga yajin aiki, kuma an shafe watanni ana cikinsa.
Ba Ibrahim da abokinsa kawai yajin aikin ya yi wa mummunan tasiri ba, gomman ɗalibai ne suka rubuto wa BBC Hausa yanayin da yajin aikin ya jefa su a ciki.
Kuma duk da cewa akwai ɗumbin jami’o’in kudi masu zaman kansu a ƙasar, ba kowane zai iya biya ba.
Ibrahim wanda a yanzu ya kama kasuwanci ka’in da na’in don rufa wa kansa asiri kafin a janye yajin aikin, ya ce yana iya bakin ƙoƙarinsa don fitar da abokin nasa daga halin da ya shiga ta hanyar yi masa nasiha.
“Aji uku muke a jami’a, ai ba zai yiwu na sa ido damuwa ta hana mu ƙarashe wahalar da muka fara ba wacce muke sa ran za mu ci ribarta a gaba,” ya ce.
End of Wasu labaran da za ku so ku karanta
A labarin da Usman Rabi'u Jibaga ya aiko daga jihar Kano ya koka kan halin da ya ce gwamnati da ƙungiyar ASUU sun jefa ɗalibai irinsa a ciki.
Ya yi zargin cewa zaman banzan da yajin aikin ya jefa mutane a ciki ya sa da yawa sun hau turbar lalacewa.
“Wannan yajin aiki ya saka wasu sun koma sata, wasu sun shiga harkar daba, wasu harkar ƙwace, gashi nan dai an saka matasanmu sun bi munanan hanyoyin da ba su dace ba duk a dalilin rashin karatu.
Ya yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen wannan yajin aiki har abada a Najeriya.
Alhaji Sulaiman Baffa daga Itas Gaɗau a jihar Bauchi, ya ce yajin aiki ya mayar da mafi yawan ɗalibai ci-ma zaune, ya sa ƙwaƙwalwarsu ba ta iya riƙe abu.
“Yajin aiki ya sa wasu daga cikin ɗalibai sun lalace, wasu sun koma shaye-shaye wasu sun koma sata da dai sauran su,” ya ce.
Saƙe-saƙe
Mubarak Yusuf daga jihar Katsina ya ce babbar matsalar da yake fuskanta a yanzu ita ce shiga damuwa da yake yi da kuma kadaici.
“Ina jin haushin rashin cigaban karatuna, na gaji da zama a gida saboda yajin aiki. Wani lokaci zuciyata na ayyana min na aikata abun da bai kamata ba, tunani kala-kala yana zuwa mini cewa na haƙura da karatu na kama wata sabgar.
Ya ce ba shi da buri irin ya ga ya yi karatu ya zama abin alfahari ga iyayensa da al’ummarsa da abokanensa.
“Lokacin yajin aiki yana farko nakan ɗan karanta wasu litattafaina saboda su rage min damuwa, ina ganin kamar yajin aikin bazai yi nisa ba.
“Amma yanzu duk wannan shauƙin ya fara fita daga zuciyata. Ina son makaranta sosai,” Mubarak ya faɗa.
Da yanzu na kammala karatu
Ishaq Gambo IG kuwa a nasa labarin da ya turo, cewa ya yi ba don irin yaje-yajen aikin da ake fama da su a ƙasar ba da tuni ya kammala karatunsa na jami’a.
“Tun a shekarar 2021 ya kamata in gama makaranta amma yanzu gani har 2022 na neman ƙarewa kuma a hakan ma babu tabbas ɗin gamawa a banan,” Ishaq ya koka.
Baya ga haka matashin ɗan garin Faskari a jihar Katsina ya ce yaje-yajen aikin ya sa sai shekarun ɗalibai su ja ta yadda za su wuce yin hidimar ƙasa da samun damar yin aiki da wuri.
“Babbar matsalar ita ce ni da wasu daga cikin abokaina muna da shekara 29 a yanzu wanda ya kamata mu gama karatunmu muna da shekara 27, amma yau gashi wankin hula yana neman ya kai ni dare.
“Babu mamaki zan gama makaranta ina da shekara 30, wanda ba lallai ba ne in samu damar zuwa bautar kasa.
Nasir Muhammad Ghali ɗalibi daga jihar Kano ya ce tun da ya fara karatun jami’a a shekarar 2018 bai taɓa yin shekara biyu cikakkiya a jere yana karatu ba tare da an tafi yajin aiki ba.
“A ƙarshen watan Satumban 2022 ya kamata na gama jami’a amma yanzu ban ma san ran da Asuu za ta janye yajin aiki ba balle na san ranar gamawa.
“Fatana shi ne Allah ya ba mu shugabanni na gari da za su damu da damuwarmu,” in ji ɗalibin.
End of Karin labaran da za ku so ku karanta
Yawan shekaru na rage damarmaki
Wasu ɗaliban kuma irin Mubarak Yusuf sun ce ya ce yajin aikin ya rusa mafarkai da burikansa.
Matashin wanda ya fara karatu a shekarar 2019 ya ce, “amma tun a zangon farko na fara fuskantar barazana ta yajn aiki, haka muka dawo gida tsawon wata takwas har kullen korona ya ƙara shafar karatun 19, haka muka yi asarar zangon karatu na shekarar baki daya sanadiyar yajin aiki, abin ya sani takaici.
“Dukkan burikana suna neman rugujewa. Ina son na kammala digiri ina da ƙarancin shekaru, ta yadda zan kammala PhD ɗina ina da shekara 30, amma yanzu wannan burin nawa ya zama tarihi, don a yadda abubuwa ke tafiya da wuya hakan ta yiwu.
“Babbar illar wannan yajin aikin shi ne shekarunmu kullum suna ƙaruwa amma karatunmu kullum baya yake komawa.
“Muna fuskantar matsalar shekaru a wurare da dama kamar NYSC da neman aiki da sauransu, duk suna da ƙa’idar shekaru.
Salihu Mu’azu shi ma ɗan jihar Katsina cewa ya yi tabarbarewa ilimi na ɓata wa matasa lokaci na cimma alkhairan rayuwarsu.
“Dubi yaran nan da suka yi jarabawar samun shiga jami’a ta JAMB, suna so su cike amman ko sun cike sai dai su yi ta jira saboda akwai wadanda aka bai wa admission suna jira, ga wasu sun fara ko aji daya ba su gama ba.
“To don Allah wannan wane irin zalinci ne? Ko don ƴaƴansu suna karatu a ƙasar waje ne su kuma sun gama nasu karatun, mu kuma ba a so mu yi ne?
“Wannan har da bakin ciki a ciki, an cutar da mu wallahi,” kamar yadda ya rubuto.