Girke-girken Ramadan: Farfesun naman rago da N3,000 kacal
Girke-girken Ramadan: Farfesun naman rago da N3,000 kacal
An wallafa
Wannan wani shiri ne da BBC Hausa take kawo muku kullum a watan azumi, don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.
A wannan bidiyo, za ku kalli gwanar girkinmu ta yau, da ke nuna mana yadda da ɗan kudi ƙalilan za a iya haɗa abinci mai rai da lafiya, don masu azumi.
Maryam Sa'idu wadda aka fi sani da Chef_ Mako_ArewaFoodie a shafukan Instagram da Tiktok, gwanar mai girki ce kuma ta nuna mana yadda ake farfesun naman rago da kuskus.
Girki ne da mai azumi, ba zai so ya wuce shi ba, idan an sha ruwa!



