Ku San Malamanku tare da Mallam Mustapha Hussani Alkantara

Ku San Malamanku tare da Mallam Mustapha Hussani Alkantara
An wallafa

Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna da Mallam Mustapha Hussani Alkantara, wanda malamin addinin Musulunci ne a birnin Kano.

Malamin ya ce ya fara karatunsa na addini kusan shekara hamsin da ta wuce a wajen malaminsa na farko, wanda kuma wan mahaifinsa ne.

Wannan malami da ya fara koyar da shi, shi ne marigayi Mallam Sule Adamu.

Ya ce a wurin marigayin ya fara komai na karatunsa na addini.

Sauran malamansa

Mallam Mustapha ya ce kasancewa wannan wan mahaifi nasa malami ne mai taƙawa da gudun abin duniya, bayan wani lokaci sai ya mika shi ga wani malamin, Mallamn Auwalu Abdullahi Alkantara, mai makarantar Islamiyya ta Nuru Zaman.

Ya ce a wannan makaranta ya yi karatun littattafai da dama, har zuwa lokacin da malamin ya rasu, kusan shekara bakwai ko takwas da ta gabata.

Ba ya ga waɗannan malaman, ya ce daga cikin manyan malaman da ya tasirantu da su akwai Mallam Salele da Mallam Ali.

Malamin ya ce a lokacin da yake koyon karatu, wani ɓangare ne na tahiya ya fi ba shi wahala.

Yanzu kuma ya ce babu inda ya fi son karantawa a Alkur'ani, kamar Suratul Yasin.