Sabbin 'yan wasa 16 ne suka fara yi wa Chelsea wasa a bana

An wallafa

Kimanin 'yan wasa 16 suka yi Chelsea wasa a karon farko a kakar 2022/23.

Kenan an doke tarihin 'yan kwallo sabbi da yawa da suka yi mata tamaula a karon farko a tarihin da aka kafa a kungiyar a 1909.

Sabbin 'yan wasa Enzo Fernandez da Noni Madueke, wadanda suka buga karawar da Chelsea ta tashi 0-0 da Fulham a Premier suka cika 16 jimilla a bana.

A kakar da 'yan wasa da dama da suka fara buga wa Chelsea kwallo ita ce a 1905/06, sune wadanda suka fara yi mata tamaula.

Sabbin 'yan wasa 28 ne suka fara yi mata wasa a kakar, shi ne tarihin da take da shi kawo yanzu

A kakar 1909/10 'yan wasa 15 sabbi suka buga mata tamaula, an kuma kara yin hakan a 2017/18.

Da yake Chelsea ta dauki sabbin 'yan wasa a bana da yawa da kuma wasu da ta gayyata daga karamar kungiyar -- ta yi amfani da 16 tun fara kakar nan.

Kenan an karya tarihin shekara 113 da kungiyar keda shi na yawan sabbin 'yan kwallo da suka fara buga mata tamaula a kaka daya.

Cikin 'yan wasa 16 da suka fara yi mata tamaula a bana ta fara anfami Conor Gallagher ranar 6 ga watan Agusta a wasan Premier da ta ci Everton 1-0.

Chelsea ta dauki Enzo Fernandez daga Benfica a matakin mafi tsada a duniya kan fam miliyan 107 a watan Janairun nan.

Fernandez shi ne ya lashe kyautar matashin dan wasa a gasar kofin duniya, wanda kasarsa Argentina ta lashe.

Chelsea wadda ta buga wasa 21 a gasar Premier League tana ta tara a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 30.

Jerin 'yan wasa 16 da suka fara buga wa Chelsea karawa a kakar 2022/23

1. Noni Madueke

Chelsea 0-0 Fulham, Premier League, 3 February 2023

2. Enzo Fernandez

Chelsea 0-0 Fulham, Premier League, 3 February 2023

3. Mykhailo Mudryk

Liverpool 0-0 Chelsea, Premier League, 21 January 2023

4. Benoit Badiashile

Chelsea 1-0 Crystal Palace, Premier League, 15 January 2023

5. Joao Felix

Fulham 2-1 Chelsea, Premier League, 12 January 2023

6. David Fofana

Manchester City 4-0 Chelsea, FA Cup, 8 January 2023

7. Bashir Humphreys

Manchester City 4-0 Chelsea, FA Cup, 8 January 2023

8. Omari Hutchinson

Chelsea 0-1 Manchester City, Premier League, 5 January 2023

9. Denis Zakaria

Chelsea 2-1 Dinamo Zagreb, Champions League, 2 November 2022

10. Carney Chukwuemeka

Chelsea 3-0 Wolverhampton Wanderers, Premier League, 8 October 2022

11. Pierre-Emerick Aubameyang

Dinamo Zagreb 1-0 Chelsea, Champions League, 6 September 2022

12. Wesley Fofana

Chelsea 2-1 West Ham United, Premier League, 3 September 2022

13. Kalidou Koulibaly

Everton 0-1 Chelsea, Premier League, 6 August 2022

14. Raheem Sterling

Everton 0-1 Chelsea, Premier League, 6 August 2022

15. Marc Cucurella

Everton 0-1 Chelsea, Premier League, 6 August 2022

16. Conor Gallagher

Everton 0-1 Chelsea, Premier League, 6 August 2022