Yadda iyayen wata yarinya suka bayar da tallafin sassan jikinta bayan rasuwarta

Asalin hoton, Family handout
Bayan harbin da aka yi wa wata yarinya mai shekara shida a India a bara, iyayenta sun yanke wata shawara ta tallafa wa wasu da gaɓoɓi ko sassan jikinta.
Bayan da ake sa ran ƙasar ta zarta China a bana domin zama ƙasar da ta fi yawa a duniya, India ta kasance ƙasa ta 62 a duniya da take bayar da tallafin sassan jiki.
BBC ta yi tafiya har zuwa ƙasar Roma, a inda aka soma wata fafutika shekaru talatin da suka gabata kan wani yaro da aka kashe da bindiga.
Rolly Prajapati na bacci salin alin a watan Afrilun bara a gidansu. Su biyar ne a gidansu inda take da ƴan uwa maza da mata a wajen Delhi.
A ɗayan ɗakin, iyayenta suna shirya abincin dare inda suka ji wata ƙara daram da kuma ihu.
A lokacin da suka je aiki, Rolly na ta kuka tana kiran iyayenta kafin ta suma
Sai da suka ga jini yana fita daga ɓangaren dama na kunnenta ne sa'annan sukasan wani abu ya faru: wani harsashe ne ya ratsa ta gidansu da ke Noida inda buge ta.

Asalin hoton, Ankit Srinivas/BBC
Sai aka garzaya da Rolly asibiti, jim kaɗan bayan haka ne aka sanar da cewa ta rasu.
Ƴan sanda a Noida sun shaida wa BBC cewa babu wani wanda ake zargi a zahiri amma suna zurfafa bincike.
Bayan an shafe kwanaki ana makoki, iyayenta sun yanke hukuncin da iyaye kaɗan a India suka taɓa yanke irinsa: wato su bayar da sassan jikinta.
Rolly ce ta zama mafi ƙarancin shekaru da aka bayar da tallafin sassan jikinta.
Mahaifinta Harnarayan Prajapati ya bayyana cewa matakin da aka ɗauka na bayar da sassan jikin ba wani abu bane da aka saba yi.

Ya bayyana cewa "Ban san me zan yi ba. Ina ta tunani a cikin dare. Na shaida wa [likita] muna buƙatar ƙarin lokacin mu yi tunani.
"Sai muka yanke shawarar mu ci gaba, inda muke tunanin cewa idan sassan cikin ƴata za su iya ceton rayuwar wani, mu yi hakan.
"Muna tunanin ƴarmu na da rai a tattare da waɗanda suke da sassan jikinta - ƴarmu za ta ci gaba da rayuwa ta hakan."
Duka ƙodojin Rolly an bayar da su ga Deb Upadhyaya mai shekara1 4, waɗanda iyayenta suka shaida wa BBC cewa wani abin al'ajabi ne da suka samu sassan jikin.

Asalin hoton, Kamlesh Upadhyaya
Sun ta jira tsawon shekaru huɗu domin samun dashen ƙoda tare da cewa "an sauya musu rayuwa" saboda ƙodar Rolly ta ba Dev sabuwar rayuwa.
Sai kuma hantar Rolly an bayar da ita ne ga wani yaron ɗan shekara shida sai kuma jijiyoyin zuciyarta ga wasu ƴara ƴan shekara ɗaya da huɗu sa'annan aka bayar da fatar idonta ga wasu mutum biyu masu shekaru 35 da 71 inda ganin su ya dawo.
Mutuwar Rolly na kama da labarin mutuwar Nicholas Green.
Yaron mai shekara bakwai na hutu a Italiya da iyalensa a watan Satumbar 1994 inda motar da yake tafiya da ita aka harbe ta a bisa kuskure.

Asalin hoton, Reg Green
Iyayensa Maggie da Reg sun yanke shawarar da su bayar da sassan jikin Nicholas.
Reg ya bayar da muhimmiyar gudunmawa tun lokacin da ake gwagwarmayar cewa a bayar da sassan jiki.
A 1993, shekara guda kafin a harbe Nicholas, kashi 6.2 cikin mutum milion guda sun rina bayar da sassan jikinsu a Italiya - zuwa 2006, adadin ya kai mutum 20.











