Amurka ta ce a tsagaita wuta a Sudan bayan kashe kusan mutum 200

An wallafa

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya tattauna da babban hafsan sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan da jagoran dakarun kai ɗaukin gaggawa, Mohammed Hamdan Dagalo yayin da ake ci gaba da kafsa faɗa tsakanin dakarun shugabannin biyu na Sudan.

Kimanin 185 ne aka kashe tun bayan ɓarkewar faɗan ranar Asabar.

Anthony Blinken ya wallafa wani saƙon Tuwita da ke cewa yana jaddada buƙatar gaggawa ga dakarun shugabannin biyu su tsagaita.

Ya nanata cewa muhimmancin haka shi ne a tabbatar da tsare lafiyar jami'an diflomasiyya da kuma ma'aikatan ba da agaji.

Rundunar jami'ai masu kayan sarki ta RSF ta amsa cewa an yi wannan tattaunawa ta wayar tarho da Mista Blinken a shafinta na sada zumunta sai dai ba ta bayar da wani tabbaci na kawo ƙarshen zaman gabar ba.

Ba a iya mutunta wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa'a uku da aka sa ba daren Litinin, inda kowanne ɓangare yake zargin ɗan'uwansa da alhakin keta yarjejeniyar.

An ci zarafin wani jami'in diflomasiyyar Tarayyar Turai a gidansa na aiki, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce an yi harbi kan gine-ginen hukumominta da gidajen ajiyar kaya da masaukan baƙinta kuma wawashe su.

An fasa gidajen wasu fararen hula kuma an far wa magidanta, sai dai rundunar RSF ta musanta hannun dakarunta.

Shugabannin sojin biyu sun kasa amincewa kan makomar Sudan, ciki har da batun shigar da dakarun RSF cikin rundunar sojin ƙasar.

Har yanzu ana jin amon tashin bindigogi a Khartoum babban birnin Sudan, duk da matsin lambar da ake ci gaba da yi wa ɓangarorin da ke gaba da juna su tsagaita faɗa.

Wata 'yar fafutuka a Khartoum, Hala Y Alkarib ta faɗa wa BBC cewa har yanzu tana iya jiyo ƙarar harbin bindigogin atilare a yankin da ke kusa da su.

"Babu inda mutum zai iya zuwa, saboda ya fi hatsari mutum ya fita waje kuma babau wata hanya da take da aminci," in ji ta, ta ƙara da cewa halin da ake ciki a Khartoum yana daɗa "taɓarɓarewa sosai".

An ba rahoton cewa dakarun sojin Sudan da mayaƙan ƙungiyar RSF ta masu kayan sarki har yanzu na ci gaba da faɗa a ƙoƙarinsu na ƙwace iko da hedkwatocin soja da ke babban birnin.

Tashar talbijin ta Al-Arabiya taba da rahoton jin ƙarar "fashewar bama-bamai da gagarumin amon bindigogi" a kusa da yankin a wayewar garin Talata.

Haka zalika, an ba da rahoton ɓarkewar faɗa a zagayen kusa da filin jirgin sama na Khartoum da sauran wurare a Omdurman da kuma Kahrtoum Bahri.

Duka ɓangarorin biyu suna iƙirarin ƙwace iko da cibiyar bayar da umarnin sojoji da kuma babban filin jirgin saman Sudan.