Girke-Girken Ramadan: Yadda ake abincin mai gyambon ciki
Girke-Girken Ramadan: Yadda ake abincin mai gyambon ciki
An wallafa
Wannan wani shiri ne da BBC Hausa ke kawo muku a kullum da azumi don bai wa mata damar gwangwaje basirarsu ta girki.
A wannan bidiyon za ku kalli yadda ake yin nau'o'i biyu na abincin da mai fama da cutar gyambon ciki (Ulcer) zai iya ci a lokacin azumi.
Maryam Sa'idu ita ce wadda BBC ta tattauna da ita kan yadda ake waɗannan nau'o'i na abinci.



