Ganawar Buhari da Sarki Charles lll, da tsuntsun yumɓu cikin hotunan Afirka na mako

An wallafa

Wasu zaɓaɓɓaɓun hotunan Afirka na mako, da na 'yan nahiyar a wasu yankunan Duniya

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Asabar kenan yayin da mutane suka taru domin kallon wasan tseren ababen hawa a Afirka ta kudu
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gasar wacce aka gudanar a birnin Cape town, an yi amfani da ababen hawa da ake kera a cikin kasar
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Lahadi lokacin bikin nuna wani film mai suna Wakanda, wanda ya samu halartar jaruman film kamar su Lupita Nyong'o da Tenoch Huerta, Danai Gururi
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, 'Yan kallo da dama sun yi wa fuskokinsu fenti a lokacin kallon film din
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani mutum riƙe da tsuntsun da ya ƙera da yumɓu a garin Gabe Bazaar na birnin Khartoum da ke kasar Sudan.
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ranar Asabar ne kuma aka gudanar da gasar harbin bindiga a birnin na Khartoum
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan matar na daga cikin matan da suka fafata a gasar
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Leah Namugerwa kenan 'yar asalin Uganda a yayin da take jawabi a taron sauyin yanayi na COP27, inda take kira ga shugabannin kasashen duniya da 'yan siyasa da su maida hankali wajen daukar matakan da suka dace kan sauyin yanayi
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu rajin kare muhalli sun halarci taron na COP27 domin roƙon shugabannin duniya da su ɗauki matakan magance sauyin yanayi
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Juma'a mutane a birnin Bamako na kasar Mali sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ɓatanci ga addinin musulunci, bayan da bidiyon wani mutum da ke zagin Al-qur'ani ya yadu a shafukan sada zumunta
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sharon Lokedi kenan 'yar asalin Kenya ke murnar lashe gasar tseren gudu ta mata da aka gudanar a birnin New York na Amurka
.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, 'Yar gwagwarmayar Kenya Elizabeth Wathuti lokacin da ta ziyarci gidan ajiye fulawoyi a birnin Nairobi Arboretum
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ranar Laraba, yayin da wannan matar ke kaftu domin shuka masara a Zimbabwe
.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yayin da al'ummar Kenya ke fama da mummunan fari, waɗannan giwayen na shan ruwa a wata rijiya mai amfani da hasken rana da aka samar a yankin Taita Taveta.
.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Ranar Laraba shugaban Najeriya ya kai wa Sarki Charles III ziyara a fadarsa da ke Buckingham a birnin Landan