Shin gwamnatin Tinubu ba ta jure wa suka ne?

Asalin hoton, fb/multiple
A yanzu haka dai akwai alamun rashin jituwa da kuma zaman ƴan marina a tsakanin waɗansu ƴan majalisar dattijan Najeriya sakamakon cire mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Muhammad Ali Ndume.
Bayanai sun nuna cewa Sanatoci daga arewacin Najeriya sun soma wani yunkuri na haɗa kansu waje guda ganin cewa duk wanda ya soki gwamnatin Tinubu ana sa kafa a shure shi.
A baya ma an dakatar da Sanata Abdul Ningi daga zauren majalisar sakamakon zargin cewa an yi cushe a kasafin kudin kasar. Zargin da majalisar ta musanta.
Ma’abota shafukan sada zumunta sun yi ta zazzafar mahawara a tsakaninsu sakamakon abin da suka ce majalisar dokokin ƙasar na cikin aljihun ɓangaren zartarwa ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Matasa da dama sun soki irin yadda babu zato ba tsammani aka cire Sanata Muhammadu Ali Ndume daga muƙaminsa na mai tsawatarwa saboda kalaman da ya yi na sukar gwamnatin Tinubu.
Abin da waɗansu suka ce, gwamnatin "ba ta iya jure wa suka" duk da cewa da dama a cikin ƴan ƙasar na ganin cewa ana cikin yanayi mara daɗi sakamakon tsadar rayuwa da ke ƙaruwa tun bayan hawan gwamnatin Tinubu da kuma yadda aka cire tallafin man fetur ba tare da wani tanadi na rage wa ƴan ƙasar raɗaɗi ba.
Faɗin ra'ayi ko suka?
Ɗaya daga cikin manyan siffofin mulkin dimokuraɗiyya shi ne ƴancin faɗin ra'ayi, wanda ake ganin babban ginshiƙi ne da ya bambanta dimokuraɗiyya da mulkin soja ko na kama-karya.
Dakta Abubakar Kari na sashen koyar da siyasa a Jami'ar Abuja ya ce: "Ƙarƙashin tafarkin dimokuraɗiyya akan sakar wa kowa mara ya faɗi albarkacin bakinsa".
Ya ƙara da cewa "Idan Ali Ndume, wanda hamshaƙin ɗan siyasa ne kuma mai riƙe da babban muƙami ya faɗi ra'ayi kuma (sanadiyyar haka) ya rasa muƙaminsa a Majalisa, to wannan ya zama naƙasu ga tafarkin demokuraɗiyya".
Dakta Kari ya bayyana cewa ba baƙon abu ba ne samun saɓanin ra'ayi a tsakanin ƴaƴan jam'iyya ɗaya a ƙasashen da ake mulkin demokuraɗiyya, sai dai ya ce wannan bai kamata ya haifar da gaba ba.
A cewar sa ana samun irin wannan saɓanin ra'ayi a ƙasashen duniya masu bin tsari na demokurɗiyya waɗanda suka ci gaba, kamar Birtaniya da Amurka, kuma hakan na taimakawa ne wajen gyara al'amura domin tafiya ta yi kyau.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A cikin watan Maris ma sai da majalisar dattijan Najeriya ta dakatar da Sanata Abdul Ningi daga jihar Bauchi na wata uku sakamakon hirarsa da BBC Hausa inda ya yi zargin cewa an cusa makudan kudaden a cikin kasafin kudin kasar ba tare da an fayyace irin ayyukan da za a yi da su ba.
Ko da yake majalisar ta musanta wannan babban zargin amma masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun nuna cewa akwai ayar tambaya a kan yadda ake aiwatar da kasafin kudin kasar.
Tun bayan hawan Bola Tinubu kan karagar mulki a shekara ta 2023, tattalin arzikin Najeriya ya kamu da masassara inda hauhawar farashin kayayyaki ke addabar al’umma inda galibin ‘yan kasar ke wayyo Allah – rana kuna, Inuwa zafi.
A yanzu haka da hukumar kiddiga ta kasar ta ce kusan watanni 18 a jere ana samun hauhawar farashin kaya a kasar a yayin da a jiya darajar Naira ta kara faduwa – ta kai naira kusan naira 1600 a kan kowacce dalar Amurka.
A farkon wannan makon ne gwamnatin Tinubu ta ce ta baiwa kowacce jiha tirelar shinkafa 20 domin rabawa talakawa sannan kuma ta ce nan gaba kadan manyan motocin sufuri masu arha ga masu karamin karfi.
Sai dai duk irin matakan da gwamnatin ta ce tana dauka domin rage radadin basu soma tasiri ba saboda bisa dukkan alamun farashin kayayyaki kullum sama yake.












